Mafarauta sun kashe ′yan Boko Haram 75 a arewacin Najeriya | Labarai | DW | 13.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mafarauta sun kashe 'yan Boko Haram 75 a arewacin Najeriya

Rahotanni daga arewacin jihar Adamawa na cewa ‘yan tauri, maharba da ‘yan banga sun kusa kai zuwa Karamar Hukumar Maiha a kokarin kwato garin gaba daya.

Wani rahoto da wata jaridar Najeriya ta buga a wannan Alhamis ya ce mafarauta sun kashe 'yan Boko Haram akalla 75 a arewacin Najeriya. Rahoton ya ce mafarautan daga garin Maiha sun fusata da yadda 'yan Boko Haram ke yawaita kashe mutane a wannan yanki. Jaridar ta Premium Times ta rawaito wani mazaunin garin na Maiha mai suna Bello Ya'u na cewa mafarautan hade da 'yan tauri da 'yan banga sun yi shiri sosai kuma sun fafata da 'yan Boko Haram inda suka halaka da yawa a cikinsu sannan daga bisani sun sake kwace garin daga hannun masu ta da kayar bayan, wadanda suka kama garin a ranar Litinin bayan wani gumurzu da dakarun gwamnati. Ita ma jaridar This Day Live a shafinta na intanet ta rawaito cewa mafarauta sun sake kwace garin a ranar Laraba.