Madugun ′yan adawar Burundi ya karbi mukami a majalisa | Labarai | DW | 30.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Madugun 'yan adawar Burundi ya karbi mukami a majalisa

Agathon Rwasa ya ce ya karbi tayin ne domin ci gaba da bada tasa gudunmawa wajen neman shawo kan rikicin siyasar kasar ta Burundi.

A Burundi majalisar dokokin kasar ta zabi madugun 'yan adawa Agathon Rwasa a matsayin mataimakin shugaban majalisar a lokacin wani zama da ta gudanar a wannan Alhamis. Wannan mataki da madugun 'yan adawar kasar ta Burundi ya dauka na karbar tayin wannan mukami ya raunana bangaren jam'iyyun adawar kasar tare da bai wa Shugaba Pierre Nkurunziza wanda aka gudanar da zabensa yau da 'yan kwanaki a cikin wani yanayi mai cike da rudani kwarin guiwa.

Da ya ke jawabi a gaban manema labarai a lokacin bikin kaddamar da majalisar a farkon wannan mako madugun 'yan adawar kasar ta Burundi wanda a baya ya yi fice wajen kalubalantar shirin tazarcen Shugaba Pierre Nkurunziza, ya bayyana cewa ya karbi wannan mukami ne domin ci gaba da bada tasa gudunmawa wajen neman gano bakin zaren warware rikicin siyasar kasar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dari a kasar a yayin da wasu sama da dubu 160 suka yi gudun hijira.