Madugun adawar Kenya ya janye takararsa | Labarai | DW | 10.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Madugun adawar Kenya ya janye takararsa

Madugun 'yan adawar kasar Kenya Raila Odinga ya sanar da kauracewa zaben shugaban kasa da ake shirin sakewa a ranar 26 ga wannan wata na Oktoba a bisa zargin hukumar zaben da rashin kawo gyara a tsarin zaben.

Madugun 'yan adawar kasar Kenya Raila Odinga ya sanar da kauracewa zaben da kasar ke shirin sakewa a ranar 26 ga wannan wata na Oktoba bayan da kotun kolin kasar ta soke zaben ranar takwas ga watan Agusta wanda shugaba Uhuru Kenyata ya lashe. 

Raila Odinga ya bayyana bukatar dage zaben na ranar 26 ga wannan wata har ya zuwa wani lokaci na gaba. Madugun 'yan adawar Kenyan ya bayyana wannan mataki nasa ne lokacin wani taron manema labarai da ya kira a wannan Talata a birnin Nairobi inda ya ce ya dauki matakin kauracewa zaben ne domin hakan shi ya fi zama alkhairi ga kasar ta Kenya ga yankin nasu dama ga duniya baki daya. 

Odinga ya kuma kara cewa alamu na nuni da cewa zaben da ake shirin gudanarwa a ranar 26 ga wannan wata zai fi wanda aka soke muni kasancewa hukumar zaben kasar ta IEBC ba ta da niyyar kawo gyara a tsarin zaben da ma sauya jami'anta ta yadda za a kauce wa sake aikata irin kura-kuran da suka yi dalilin soke zaben na ranar takwas ga watan Oktoba.