Madugun adawan Zimbabuwe ya rasu | Labarai | DW | 15.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Madugun adawan Zimbabuwe ya rasu

Al'ummar kasar Zimbabuwe na ci gaba da jimamin mutuwar madugun adawa kuma tsohon Firaiministan kasar Morgan Tsvangirai bayan da ya sha fama da cutar kansar hanta.

Simbabwe Morgan Tsvangarai verhaftet (AP)

Tsvangarai ya rasu a wani asibiti da ke a Afrika ta Kudu a wannan  Laraba. Elias Mudzuri daya daga cikin jagorin jam'iyyar adawa ta MDC ne ya sanar da mutuwar.

Tsvangarai shi ne mutumin da ya kafa jam'iyyar MDC a shekarar 2000, ya kuma kwashi shekaru da dama ya na adawa da Robert Mugabe tsohon shugaban kasar ta Zimbabuwe. Madugun adawan ya sha jagoranta gangami don kalubalantar mulkin Mugabe na wancan lokacin lamarin da ya kai shi ga zaman gidan kurkuku a sau da yawa. Marigayin ya rasu ya na da shekaru sittin da biyar.