Madagaska ta nemi tallafin kasa da kasa | Labarai | DW | 28.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Madagaska ta nemi tallafin kasa da kasa

Kasar dai ta yi kira ga al'ummomin kasashe su tallafa mata bayan da a farkon wannan wata guguwa hade da ambaliya ya lalata wannan kasa inda mutane 68 suka rasu.

Madagaska ta nemi tallafin kasa da kasa Gwamnatin kasar Madagaska ta yi kira ga al'ummomin kasa da kasa su tallafa mata bayan da a farkon wannan wata guguwa hade da ruwan sama mai karfin gaske ya lalata wannan kasa da ke zama wani tsibiri a tekun Indiya da haddasa sara da ta kai kimanin dalar Amirka miliyan arba'in.

Mutane 68 ne dai suka rasa rayukansu yayin da 130,000 suka kauracewa muhallansu lokacin wannan bala'in guguwa ta Chedza ta afkawa tsibirin Madagaska a ranar 16. ga watan Janairu kamar yadda ma'aikatar da ke lura da afkuwar bala'oi ta kasar ta bayyana.

Har ila yau wannan bala'in guguwar ya shafi kasashen Malawi da Mozambique da Zimbabuwe cikin irin bala'oin da suka shafi wadannan kasashe cikin 'yan shekarunnan, tafkuna da koguna sun tumbatsa tare da sanya mabaliyar ruwa da ta jawo lalacewar hanyoyi da gidaje da amfanin gonaki.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Pinado Abdu Waba