1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta sake ta'azzara a Madagaska

Zainab Mohammed Abubakar
July 5, 2020

Madagaska ta kafa dokar hana fita a babban birnin kasar, Antananarivo, sakamakon sake barkewar annobar corona watanni biyu bayan sassauta dokar hana fita.

https://p.dw.com/p/3epIG
Madagaskar Corona-Pandemie polizei
Hoto: Getty Images/AFP/Rijasolo

Daga wannan Lahadin ce aka sake sanar da killace gundumar Analamanga, yankin da fadar gwamnatin ke ciki. Kuma daga gobe Litinin babu shiga ko fita a wannan yanki baki dayansa har zuwa ranar 20 ga watan Juli.

A kwanakin da suka gabata dai gomman mutane ake samu da cutar, amma a wannan Asabar kadai mutane sama 200 aka tabbatar da cewar sun kamu da COVID-19, bayan gwajin da aka yiwa mutane 675.

Baki daya kuma an gudanar da gwaji a kan mutane dubu 24 a wannan tsibirin. Yanzu haka dai mutane 2,728 ne suka kamu da corona, ciki har da 29 da suka mutu.