Faransa ta yi nadama kan rikicin Ruwanda
May 27, 2021Talla
Yayin wata ziyara a Kigali babban birnin kasar Ruwanda, Shugaba Macron ya ce Faransa ta dauki nauyin abin da ya faru tare da neman yafiya. Sai dai shugaban Faransa bai nemi gafara a hukumance ba, ya yi kalaman ne a wurin da aka binne mutane 250,000 da aka yi wa kisan kiyashi a birnin Kigali.
A watan Yulin shekarar 1994 ne Shugaban Ruwanda Paul Kagame ya jagoranci wata rundunar da ta kawo karshen kisan kiyashin a watan Yunin 1994, bayan da mayakan kabilar Hutu suka kashe 'yan kabilar Tutsi 800,000 cikin kwanaki 100 ana ba ta kashi.