Macron da Le Pen sun zama zakarun Zaben Faransa | Labarai | DW | 23.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Macron da Le Pen sun zama zakarun Zaben Faransa

Alkaluman da kafofin watsa labarai suka bada sun nunar da cewar Emmanuel Macron da Marine Le Pen sun haye zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Faransa sakamakon rinjayen kuri'un da suka samu a zagayen farko..

Sakamakon zagayen farko na zaben kasar Faransa ya bayyana Emmanuel Macron da kuma mai kyamar bakin nan wato Marine Le Pen a matsayin wadanda za su fafata a zagaye na biyu na zaben da zai gudana a ranar 7 ga watan gobe na Mayu. Emmnuel Macron dan shekaru 39 a duniya ya samu kashi 24 na zaben yayin da Marine Le Pen ta sami kashi 22. 

Ana ganin sakamakon karshe na zaben Faransar makonni biyun da ke tafe, a matsayin zabe mai tasiri a nahiyar Turai dama sauran kasashen duniya. Zaben na  ya gudana ne karkashin tsauraran matakan tsaro sakamakon hare-haren ta'addanci da kasar ta yi fama da su a watannin baya-bayannan.

Akalla dai an sami kashi 78 cikin darin wadanda suka yi rajista da suka yi zaben. 'Yan takara hudu ne dai suka fi daukar hankali yayin wannan zabe, biyu masu matsanancin ra'ayi sai kuma wasu biyu masu ra'ayin mazan jiya.

 

Sauti da bidiyo akan labarin