Macky Sall ya lashe zaben Senegal | Labarai | DW | 01.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Macky Sall ya lashe zaben Senegal

Hukumar zaben kasar Senegal ta sanar da Shugaba Macky Sall a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata.

Shugaba Macky Sall ya ci zaben ne da kashi 58% na kuri'un da aka kada a cewar hukumar, inda zai sake mulkin kasar na shekaru biyar nan gaba. Abokin takarar Macky Salla, tsohon firamnista Idrissa Seck, ya zo na biyu da kashi 20.5%

Sai dai ba za a sahale wa Shugaba Macky Sall nasarar ba, sai har kotun tsarin mulkin kasar ta tantance tare da tabbatar tsari da kuma abin da hukamar ta sanar.

Jam'iyyun hamayya a Senegal din dai sun yi watsi da sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayyana.