Mace za ta zama shugabar Tanzaniya | Labarai | DW | 18.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mace za ta zama shugabar Tanzaniya

Jama'a a ciki da wajen Tanzaniya na ci gaba da aike wa da sakon ta'aziyya bisa mutuwar Shugaban kasar John Magufuli.

A yammacin Larabar nan ce dai Mataimakiyar Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan ta sanar da cewa Shugaba Magufuli ya rasu a birnin Dar es Salaam. Sai dai sabanin cutar corona da ake ta rade-radin cewa ita ce ta kama shi da ba a ganinsa a bainar jama'a a 'yan kwanakin nan, mataimakiyar shugaban kasar ta ce Magufuli ya mutu a sakamakon wani nau'i na ciwon zuciya wanda ya kwashe shekaru fiye da 10 yana fama da shi.

A bisa tsarin mulkin Tanzaniya dai yanzu mataimakiyar shugaban kasa Samia Suluhu Hassan ce za ta maye gurbin Shugaba Magufuli, kuma za ta ja ragamar kasar har zuwa shekara ta 2025 lokacin da za a gudanar da sabon zabe.