Mace-mace a harin da aka kai wa Haftar | Labarai | DW | 05.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mace-mace a harin da aka kai wa Haftar

Madugun 'yan tawayen Libya Janar Haftar ya sha alwashin daukar fansar harin kunar bakin waken da aka kai gidansa da ke Benghazi, ya kuma kashe mutane da dama.

Wani harin kunar bakin wake da aka kaddamar a gidan madugun 'yan tawayen Libiya kana tsohon janar Khalifa Haftar ya yi awaan gaba da rayukan mutanr hudu ciki kuwa har da wanda ya dana bam din. Wasu karin mutane uku sun samu raunuka bayan da wani dan takife ya durfafi gidan Hafter da ke Benghazi da wata mota da ke makare da bama-bamai.

Babu dai wanda ya dauki alhakin wannan hari ya zuwa yanzu. sannan ana tababa kan cewa shi tsohon janar din na Libya Khalifa Haftar ya samu rauni. Sai dai kuma bayan da ya tsallake rijiya da baya,madugun yan tawayen na Libiya,Janar Haftar,ya sha alwashin mai da mummmunan martani.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da kotun tsarin mulkin kasar ta Libya za ta fayyace a wannan alhamis halarci ko rashin halaccin zaben da aka yi wa firaministan kasar Ahmad Muaiteeq.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar