Mabarata na cikin mawuyacin hali | Zamantakewa | DW | 24.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Mabarata na cikin mawuyacin hali

Mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu, ya kalubalanci matakin gwamnatin jihar na haramta bara ba tare da samar wa Mabaratan mafita ba.

Tun kafin akai ga nada Muhammad Sunusi na 2 a matsayin sarki, gwamnatin Kano ta lashi takobin kakkabe bara daga jihar ta hanyar yin dokar da ta bata damar bin almajirai ana kamasu. Sai dai wasu kalamai da sarkin ya yi sun kalubalanci wannan mataki na haramta bara. Sarkin na Kano ya bayyana cewar ko kadan bai kyautu a hana mutane bara ba, matukar ba'a samar musu da wata madogara ba. Domin idan ka hana mutum bara kuma baka ba shi abin da zai dogara da shi ba, zai iya shiga harkar sata.

Sarki Muhammad Sunusi na 2 ya ce, shi kansa gwamnati ta yi kokarin hana shi taimakawa almajirai da talakawa matakin da ya ce bai amince da shi ba.

Sai dai kuma a nata bangaren, gwamnatin Kano ta ce ba zata mayar da martani kan wannan batu ba har sai ta kammala nazari tukunna, kamar yadda Tijani mai Lafiya mashawarcin gwamnan Kano kan al,amuran da suka shafi masarautar Kano ya nunar.

Sauti da bidiyo akan labarin