Ma'auratan da aka daure kan yin rawa a Iran | Labarai | DW | 01.02.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ma'auratan da aka daure kan yin rawa a Iran

Ma'auratan biyu za su shafe shekaru 10 a gidan yari, bayan da kotun musulunci ta same su da laifin wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta suna rawa kuma amaryar ba ta yi lullubi ba.

Ma'auratan da aka daure kan yin rawa

Ma'auratan da aka daure kan yin rawa

Wata kungiyar kare hakkin jama'a ta Amirka, ta ce tun a watan Nuwamban 2022 aka kama ma'auratan Amir Mohammad Ahmadi mai shekaru 22 da Amaryarsa Astiyazh Haghighi mai shekaru21 bisa zargin saba dokokin shari'a na yin rawa babu lullubi a bainar jama'a.

Tun a tsakiyar watan Satumban shekara ta 2022, matasa na ta gudanar da zanga-zangar adawa da tsauraran dokokin gwamnati a Iran, bayan mutuwar wata matashiya mai suna Mahsa Amini a hannun 'yan sanda bayan da aka tsare ta kan saba ka'idar sa sutura ta addini.