Luguden wutar dakarun gwamnati a Siriya | Labarai | DW | 07.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Luguden wutar dakarun gwamnati a Siriya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa al'amura ka iya rincabe wa a Siriya bayan kwashe tsahon sa'o'i 48 sojojin gwamnati na luguden wuta a yankunan Idlib da gabashin Ghuta.

Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da luguden wuta a yankunan Idlib da Ghuta

Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da luguden wuta a yankunan Idlib da Ghuta

Hare-haren dai na kara ta'azzara ne a dai-dai lokacin da Majalisar ta Dinkin Duniya ke gudanar da bincike kan wanda ya kai hari da makamai masu guba a yankunan da ke hannun 'yan tawaye, wanda kuma ya hallaka fararen hula. Rahotanni sun nunar da cewa akalla mutane 70 ne suka hallaka a yankin da ke hannun 'yan tawayen wanda ke kusa da babban birnin kasar Siriyan Damascus cikin wannan mako da gwamnati ke kara zafafa kai hare-hare.