Liu Xiaobo babban dan fafutika ya rasu | Labarai | DW | 13.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Liu Xiaobo babban dan fafutika ya rasu

Dan kasar China na farko wanda ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 2010, ya rasu a wannan Alhamis din yana dan shekaru 61 da haihuwa.

China Liu Xiaobo, Aktivist 1995 (Reuters/W. Burgess)

Marigayi Liu Xiaobo babban dan fafutika na kasar Chaina.

Sakataran harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ya nuna girmamawarsa ga marigayi Liu,  inda ya ce ya kasance babban dan adawa mai fafutika na kasar ta China wanda ya rasu bayan da ya yi fama da cutar dafi. Marigayin ya sadaukar da rayuwarsa ce wajen ci gaban kasarsa ta China da kuma ci gaban al'umma.

Cikin wata sanarwa Sakataran harkokin wajen na Amirka ya yi kira ga hukumomin kasar ta China da su saki uwargidan marigayin Liu Xia daga tsaron da ake yi mata a cikin gidanta tare da barinta ta fita daga kasar ta China kaman yadda take fata. Marigayin Liu ya rasu ne ba tare da mulkin na komunisanci na kasar ta China ya barshi ya yi sauran rayuwarsa a kasashen waje cikin inci kaman yadda ya yi fata ba.