Littattafan harshen Tangale a Jihar Gombe | Zamantakewa | DW | 12.03.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Littattafan harshen Tangale a Jihar Gombe

Farfesa Hermann Jungraithmayr ɗan ƙasar Jamus ya wallafa littattafan a harshen Tangale

A farkon wannan wata na Maris a garin Kaltungo na jihar Gombe dake arewacin tarayyar jeriya aka gudanar da bukin ƙadamar da wasu littattafai guda uku a harshen Tangale. Wani ɗan ƙasar Jamus Farfesa Hermann Jungraithmayr ya wallafa waɗannan littattafan da suka ƙunshi tatsuniyoyi, almara da karin magana da kuma tarihin ƙasar Tangale tare da camfe- camfe na wannan al´uma.

Ita dai alu´mar Tangale dake a jihar ta Gombe, al´uma ce dake da ɗinbim tarihi mai ban sha´awa da kuma mamaki, saboda haka Turawan mulki mallaka sun yi ta rubuce-rubuce game da al´adun wannan al´uma.


Mawallafi: Mohammad Awal

Edita: Tijani Lawal

Sauti da bidiyo akan labarin