Likita a Sudan ta Kudu ya samu yabon MDD | Labarai | DW | 25.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Likita a Sudan ta Kudu ya samu yabon MDD

Evan Atar Adaha dan shekaru 52 da ke kula da asibiti daya tilo a yankin arewa maso gabashi na yankin Maban ya rika daukar kasadar siyar da rai don tallafar al'umma.

Tuberkolose (picture-alliance/dpa)

Marasa lafiya a wani asibitin kudancin Dafur

Wani likita dan kasar Sudan ta Kudu ya samu lambar yabo ta hukuma da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya bayan da ya kwashe kusan shekaru 20 yana taimakon mutane da ke zama marasa lafiya a kasarsa da ke yankin gabashin Afirka wacce ke fama da tashe-tashen hankula. An bayyana wannan likita ne da samun wannan gagarumar girmamawa bayan da ya kula dubban marasa lafiya wadanda ke gujewa tashe-tashen hankula da ma gudun tsira da rai.

Evan Atar Adaha dan shekaru 52 da ke kula da asibiti daya tilo a yankin arewa maso gabashi na yankin Maban ya samu lambar yabon da ake kira Nansen Refugee Award a Turance saboda yadda ya sadaukar da rai wajen taimakon rayukan al'umma duk da cewar a lokuta da dama yana daukar kasada da ka iya sanadi na rasa ransa a cewar MDD.