Libiya: Za a ci gaba da yin yaki in ji Janar Haftar | Labarai | DW | 22.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libiya: Za a ci gaba da yin yaki in ji Janar Haftar

Jagoran 'yan tawaye na Kasar Libiya janar Khalifa Haftar wanda ke rike da yankin gabashi na Libiyar ya shaida wa shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron a birnin Paris cewa ba za a daina yin yakin ba.

Haftar ya ce  har yanzu ba a samu kyakyawan hali da yakamata ba a saka hannu hannu a kan yarjejeniyar tsagaita wuta a gewayen Tripoli. Sai dai ya ce za a iya sake komawa kan tebrin shawarwari domin samun masalha a game rikicin da suke yi da gwamnatin Tripoli da ke samun goyon bayan kasashen duniya.