Libiya ta soma bincike kan cinikin bayi | Labarai | DW | 19.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libiya ta soma bincike kan cinikin bayi

Mahukuntan kasar libiya sun sanar a wannan Lahadi da soma bincike a game da batun cinikin bayi da tashar talabijin ta CNN ta nuna a cikin wani rahoton bincike da ta gudanar. 

 A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na facebook a wannan Lahadi, Ahmed Metig mataimakin Firayin Ministan gwamnatin hadin kan kasar ta Libiya wacce kasashen duniya suka amince da ita, ya nuna takaicinsa da samun labarin cinikin bayin a kasarsa. Ya ce sun sa a gudanar da bincike kan mutanen da ke da hannu a cikin lamarin domin gurfanar da su a gaban kuliya. 

Kasashen duniya da dama ne musamman na Afirka sun nuna takaicinsu bayan bayyanar wannan labari na cinikin bayi a Libiya wanda ya soma haifar da zanga-zanga a wasu kasahen. Tuni ma dai Shugaba mahamadou Issoufou na Nijar ya sanar da saka wannan batu a taron koli na hadin gwiwar Kungiyar Tarayyar Afirka da ta Tarayyar Turai da zai gudana a karshen wannan wata a birnin Abidjan na Côte d 'Ivoire.