1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya ta shiga rudani kan fitar da man fetur

March 9, 2014

Mahukuntan Libiya sun yi barazanar tarwatsa wani jirgin ruwa da bam saboda dakon man fetur ta hanyar da ta saba ka'ida

https://p.dw.com/p/1BMXj
Hoto: picture-alliance/dpa

Firaminista kasar Libiya Ali Zeidan ya yi bazanar cewa zai ba da umurnin tarwatsa jirgin ruwa mai dauke da tutar Koriya ta Arewa, muddin ya fito da man fetur daga yankin gabashin kasar ta hanyar da ta saba ka'ida. Firamnistan ya ce ya ba da umurnin kama jirgin ruwan.

Jirgin ruwan yana yankin da ke hannun 'yan aware masu adawa da gwamnati kasar, wadanda suka ce gwamnati ba ta isa hana komai ba. Cikin watan Agusta 'yan tawayen suka kama tashoshin jiragen ruwa uku a yankin gabashin kasar.

Gwamnatin kasar ta Libiya tana asarar makudan kudade saboda yadda 'yan tawaye masu dauke da makamai suka kassara hanyoyin fitar da man fetur, abin da kasar ta dogara da shi wajen samun kudaden shiga. Kasar da ke yankin arewacin nahiyar Afirka ta fada cikin rudani tun bayan juyin-juya halin shekara ta 2011, da ya kawo karshen gwamnatin Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh