Libiya ta kama masu cuwa-cuwan mai a teku | Labarai | DW | 30.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libiya ta kama masu cuwa-cuwan mai a teku

Kasar Libiya ta kama tankunan mai na kasashen ketare a gabar ruwanta, tare da tsare ma'aikatan da ke cinikin bayan fage biyo bayan bata kashi da suka yi da hukumomi a bakin teku.

Hukumomi a kasar Libiya sun tabbatar da kwace wasu tankunan mai guda biyu da ke dauke da tutocin kasashen ketere tare da tsare wasu da ke da alaka da tankunan. An yi bata kashi tsakanin jami'an tsaro da mutanen da ake zargin suna sumogal na mai din ta baraubiyar hanya.

A cewar Janar Ayoub Qassem da ke jagorantar masu tsaron gabar tekun kasar ta Libiya, wadanda ake zargin suna fasakorin man na dauke da manyan makamai, wannan ya sa suka dau tsawon sa'o'i uku suna musanyar wuta a tsakaninsu. A kokarin daukan man ne jami'an kula da gabar teku suka warware tufkarsu, inda suka samu daya daga cikin tankunan man da ya kai tone dubu 3,330 yayin da daya tankin mai daukan mai tone dubu 1,236.

Qassem ya kuma bayyana cewa tankunan man da aka kama, na dauke da tutar kasashen Ukraine da Kwango, man fetur dai shi ne babban arzikin karkashin kasa da Libiya ke dogaro da shi.