Libiya ta ba da umarnin daukar matakin soji kan tankar jigilar mai | Labarai | DW | 10.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libiya ta ba da umarnin daukar matakin soji kan tankar jigilar mai

A wani matakin kawo karshen mamayar tashoshin jiragen ruwa da 'yan tawaye suka yi, majalisar Libiya ta kafa dokar samar da wata rundunar da za ta kai dauki.

Majalisar dokokin Libiya ta ba da umarnin kafa wata rundunar soji don kawo karshen mamayar da 'yan tawaye suka yi wa tashoshin jiragen ruwa na dakon man fetir, bayan da wani jirgi ruwa dauke turar kasar Koriya ta Arewa ya yi lodin danyan mai a daya daga cikin tashoshin jirgin rua da ke hannun 'yan tawaye. Kakakin majalisar Omar Himeidan ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa a cikin mako guda sojojin za su fara wannan aiki kamar yadda dokar majalisar ta tanada. Yanzu haka sojojin ruwa Libiya sun yi wa jirgin ruwan kawanya a wajen tashar jirgin ruwa.

A wani labarin kuma wani babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa Libiya na fuskantar barazanar mummunan tashin hankali sakamakon karuwar rigingimu a fadin kasa cikin watanni uku da suka gabata. Tarek Mitri da ke zama wakili musamman na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya fada wa kwamitin sulhu a wannan Litinin cewa halin tsaro a Libiya na ci gaba da tabarbarewa yayin da ake kara nuna rashin gamsuwa ga shirye-shiryen siyasar kasar. Mitri ya ba da misali da harin da harin masu bore suka kai kan ginin majalisar dokoki a ranar biyu ga wannan wata suna neman da a rushe ta. Sai kuma fadace fadace tsakanin kungiyoyin da ke gaba da juna a yammacin birnin Tripolis da yankin kudu da kudu maso gabashi. Kifar da Muammar gaddafi a karshen shekarar 2011, ta bar kasar ba bu wata tsayayyar gwamnati, sannan rundunonin soji da 'yan sanda sun yi rauni.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Pinado Abdu-Waba