Libiya: Sake bude wuta tsakanin sojan gwamnati da na Haftar | Labarai | DW | 12.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libiya: Sake bude wuta tsakanin sojan gwamnati da na Haftar

Gwamnatin hadin kan kasa a Libiya ta zargi dakarun da ke biyayya ga Khalifa Haftar da karya kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu suka cimma a albarkacin bukukuwan Sallah.

A Libiya an ji karar harbe-harben rokoki a babban filin saukar jiragen saman Mitiga da ke wajen birnin Tripoli, lamarin da ya kara haifar da fargaba ga al'ummar kasar a yayin da suke cikin bukukuwansu na babbar Sallah.

Sai dai a nasu bangare dakarun da ke biyayya ga Khalifa Haftar sun musanta kai harin, inda suka zargi sojojin da ke biyayya ga gwamnatin kasar da saba yarjejeniyar. Sai dai tuni manyan kasashen duniya ciki har da Amirka da Faransa suka jaddada bukatarsu ta dorewar kwarya-kwaryar yarjejeniyar  ta tsagaita wuta da aka cimma karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.