Libiya na kai hari a kan ′yan adawa | Labarai | DW | 25.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libiya na kai hari a kan 'yan adawa

Firaministan Libiya ya ce gwamnatinsa ce ke da alhakin harin da aka kai a filin jiragen sama na Tripoli babban birnin kasar da ke karkashin ikon 'yan adawa.

Shafin sadarwa na Internet din Firaminista Abdullah al-Thinni ya ruwaito shi yana mai cewa sojojin saman kasar suka kai hari a filin sauka da tashin jiragen sama da ke birnin na Tripoli. Bayanin na Thinni na zuwa ne bayan da jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Libiyan Bernadino Leon ya bukace shi da ya kawo karshen hare-haren da sojojin gwamnati ke kaiwa ta sama da jiragen yaki a kan 'yan adawa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal