Libiya: Masunta sun gano gawarwaki a Teku | Labarai | DW | 18.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libiya: Masunta sun gano gawarwaki a Teku

Wasu masunta a Libiya sun gano gawarwaki 28 a cikin teku kusa birnin Sabratha. Hukumomi a kasar sun ce mutanen sun mutu ne sakamakon rashin ruwan sha da abinci gabannin nutsewarsa.

Kwamandan kula da tsaron sashin cikin gida a Libiya Ahmaida Khalifa Amsalam ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Reuters cewa an binne gawarwakin da masuntan suka gano cikin ruwa a rami guda ciki kuwa har da mata hudu.

A tun bayan juyin juya halin da ya kifar da mulkin tsohon shugaban Libiya Muammar Gaddafi a shekara ta 2011, kasar ta zamo kofa ga bakin haure sama da dubu 150 a duk shekara suna silalewa ta ruwa zuwa nahiyar Turai.