1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lesotho ta bi sahun kasashen da ke fama da annobar COVID-19

Zulaiha Abubakar MNA
May 13, 2020

Ma'aikatar lafiya a Lesotho ta sanar da labarin billar annobar Coronavirus a wannan Larabar, biyo bayan gwajin lafiya da jami'an jinya suka gudanar kan wasu mutane 18 da suka dawo daga Saudiyya da Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/3cAWJ
Firaiministan kasar Lesotho Thomas Thabane yayin wani taro na musamman kan corona
Firaiministan kasar Lesotho Thomas Thabane yayin wani taro na musamman kan coronaHoto: AFP/M. Molise

Ma'aikatar lafiyar kasar Lesotho ta shaidawa manema labarai cewar wanda aka samu da cutar ya kasance dalibi a kasar Saudiyya, al'amarin da ya bayyana bayan firaiministan kasar Thomas Thabane ya sanar da sassauta dokar kulle a makon da ya gabata.

Kasar ta Lesotho ta yi gaggawar daukar matakan hana shigowar cutar corona daga kasar Afirka ta Kudu inda akalla mutane dubu 11 da 350 suka kamu da cutar bayan wasu 206 sun rasa rayukansu.

Hakan ta sa yanzu kasar Lesotho ta shiga sahun kasashen Afirka da annobar ta yadu a cikinsu.