Legas: Sabuwar tukunyar gas ta girki | Himma dai Matasa | DW | 05.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Legas: Sabuwar tukunyar gas ta girki

Wani matashi a Najeriya Injiniya Opeyemi Oshowe daga jihar Legas ta Najeriya, ya kirkiro wata sabuwar tukunyar Gas ta girki mai sauki ga jama’a.

Tunkunyar gas din dai a kalla ta fada gidaje sama da dubu daya da daribiyar bayan  amfani da matasa da ke taimaka masa a kamfanin nasa, mai suna Fitco-Tech a birnin Legas.

Bayan kammala karatunsa jami'ar Lagos, Injiniya Opeyemi Oshowe ya zartar da hukuncin yin dogaro da kai a maimakon aiki da gwamnati.

A kwazon da ya ke nunawa ta wannan sabuwar dabara ta tukunyar gas cikin sauki, ya samu kyautar yabo da lambar girma a cikin gida Najeriya da waje. Inda har kungiyar GIZ ta Jamus ta tabbatar masa da lambar girma.

"Wannan tukunyar gas da na kirkiro ta na da wata na'ura da zata magance tsiyayar gas ta kowace siga don gudun gurbata yanayi ko gobara a cikin gida. Wannan dai wani kalubale ne ga matasa a Najeriya".