Lavrov: Zargi na da Trump ba hujja
May 18, 2017Talla
Duk da cewar Sergei Lavrov bai bayyana abubuwan da suka tattauna da shugaba Trump din ba, Mr Lavrov ya ce bai fahimci zancen sirrin da ake kururutawa ba, musamman kan batun haramta shiga jirage da kwamfutocin Laptop saboda gudun hare-haren ta'adda.
Watanni biyu da suka gabata ne dai Amirka ta bayyana matakin haramcin shiga jirage da komfutocin gami da wasu na'urori daga kasashen yankin gabas ta tsakiya saboda dalilai na tsaro.
A cikin wannan makon ne dai jaridar Washington Post, ta yi zargin musayar bayanan sirri tsakanin shugaban Amirkan da kuma ministan harkokin wajen na Rasha, zargin da Lavrov ke cewa tamkar lokacin tsarin Komunisanci ne na baya a Rasha.