1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lauyan mai batanci ga Islama ya gudu daga Pakistan

Yusuf Bala Nayaya
November 3, 2018

Matar nan Kirista da aka yi shari'arta da ta shafi yin batanci ga addinin Islama aka kuma ba da umarnin a sake ta, bayan kwashe shekaru takwas a gidan kaso a Pakistan, kawo yanzu lauyanta ya tsallake daga kasar.

https://p.dw.com/p/37cYO
Saif-ul-Mulook
Hoto: Getty Images/A. Qureshi

Dan uwa ga Asia Bibi wato James Masih, ya bayyana a wannan  Asabar cewa lauyan 'yar uwarsa Saiful Malook, ya fice daga Pakistan ba tare da ba da wasu bayanai ba, baya ga cewa rayuwarsa na fiskantar barazana an kuma yi kokari na samunsa a waya abin ya ci tura.

A ranar Laraba ne dai kotu ta sallami Bibi inda ta ce a cire ta daga gidan kaso abin da ya harzuka zukatan 'yan fafutikar Islama da ke neman ganin an yanke mata hukuncin kisa.