1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laurent Gbagbo na gurfana gaban kotun ICC

Mouhamadou Awal BalarabeJanuary 28, 2016

Kotun kasa da kasa ta ICC na zargin tsohon shugaban Côte d' Ivoire Laurent Gbagbo da ruruta wutar rikicin siyasa da ta barke bayan zaben shugaban kasa na 2010.

https://p.dw.com/p/1Hl1j
Elfenbeinküste Präsident Laurent Gbagbo
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kooren

Tsohon shugaban Côte d' Ivoire Laurant Gbagbo Zai gurfana a wannan Alhamis a gaban kotun hukunta manyan laifukan yaki da ke birnin The Hague, domin wanke kansa daga zargin da ake yi masa na marar hannu a yakin basasa da kasarsa ta fusakanta a shekara ta 2010. Shi ne dai ya kasance wani wanda ya taba rike babban mukami na farko a duniya da zai fuskanci shari'a a wannan kotu ta kasa da kasa wacce aka kafa tun a shekaru 13 da suka gabata.

Fiye da mutane miliyan uku ne suka bakwancin lahira a rikicin siyasa da ya barke a Côte d´Ivoire, bayan da Gbagbo ya ki amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasa na 2010 wanda Alassane Ouattara ya lashe.

Babbar mai shigar da kara ta kotun ICC, Fatou Bensouda ta bayyana cewar wannan shari'ar za a yi ta bisa gaskiya da adalci.

"Bincike kan rikicin Côte d' Ivoire zai duba bangarori biyu da abin ya shafa. Ofishina ba zai nuna son kai ba. Tabbas mun fara bincike, amma kuma ba za mu iya bayyana muku inda muka kwana ko dabarun da muke amfani da su ba. Muna yinshi ne cikin sirri kamar yadda shari'a ta tanada."

F