1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Larijani ya tsaya takarar shugabancin Iran

Mouhamadou Awal Balarabe
May 15, 2021

Tsohon kakakin majalisar dokokin Iran Ali Larijani mai matsakaicin ra'ayin mazan jiya kuma mai goyon bayan yarjejeniyar nukiliya, ya sanar da takararsa a zaben shugabancin kasa da zai gudana a ranar 18 ga watan Yuni.

https://p.dw.com/p/3tQWE
Ali Larijani - iranischer Parlamentspräsident
Hoto: icana.ir

Shi dai Larijani wanda ya kusa cika shekara 64 a duniya kuma ya yi ta jan kafa wajen bayyana aniyarsa, ya jira har zuwa ranar karshe da doka ta tanada wajen mika takardarsa ta takara a ma’aikatar cikin gidan Iran. Wannan dai shi ne karo na biyu da zai tsaya takarar shugaban kasa, baya ga na zaben 2005, wanda mai tsattsauran ra'ayin mazan jiya Mahmoud Ahmadinejad ya lashe.

A yanzu haka Ali Larijani da ke fada a ji a fagen siyasar Iran, shi ne mai ba da shawara ga Jagoran Musulunci kasar Ayatollah Ali Khamenei. A lokacin da ya shugabanci majalisar dokoki, Larinaji ya kasance daya daga cikin manyan abokan Shugaba mai barin gado, Hassan Rohani, wanda ya sa aka kulla yarjejeniyar nukiliyar Iran a 2015.

Ana jin cewa makomar shirin na nukiliya za ta taka rawa a yakin neman zaben Iran baya ga batun tada komadar tattalin arziki da inganta zamantakewar al'ummar Iran.