Lambar yabo ta Nobel ga masana kimiyar Chemistry | Labarai | DW | 07.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lambar yabo ta Nobel ga masana kimiyar Chemistry

Aikin da suka gudanar ya bude sabuwar kofa a laluben hanyoyin yaki da cutar Kansa ko cutar daji, wacce ta zama babban kalubale a fannin lafiya.

Wadannan masana dai su ne Tomas Lindahl dan asalin Sweden da Paul Modrich dan Amirka sai Aziz Sancar dan asalin kasar Turkiya. An dai basu lambaobin yabo ta nazari kan kwayoyin halitta na DNA. Aikin da suka gudanar ya bude sabuwar hanya ta laluben hanyoyin yaki da cutar Kansa ko cutar daji.

Kyautar da aka basu ta kai kiyasin kudi Dala dubu dari tara da sittin. Za dai a ci gaba da bada wadannan lambobi na yabo a ranar Alhamis, inda za a bada lambar yabon ta Nobel kan adabi a ranar Alhamis sai ta zaman lafiya a ranar Juma'a da ta tattalin arziki a ranar Litinin.