Lambar yabo ta BOBS ga marubutan fafutuka | Labarai | DW | 03.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lambar yabo ta BOBS ga marubutan fafutuka

Wata 'yar kasar Bangaladash na daga cikin wadanda suka lashe kyautar masu fafutuka ta kafar sadarwa ta Internet wato "THE BOBS" da DW ke bayarwa a ko wace shekara.

Kyautar DW ta The Bobs ta 2015

Kyautar DW ta The Bobs ta 2015

Wani dan gudun hijira daga kasar Siriya na daga cikin wadanda suka lashe kyautar fitattun masu fafutuka a shafin Internet na Blog da tashar DW ke bayarwa duk shekara wanda ta yi wa lakabi da "THE BOBS". Sauran wadanda suka lashe wannan kyauta sun hadar da wani dan Mexico da kuma wata 'yar kasar Bangaladash da ke fafutuka ta kafar sadarwar Internet ta hanyar yin kasada da rayuwarta domin yaki da muzgunawa da sunan addini. Alkalan gasar karo na 11 sun bayyana sunan Rafida Bonya Ahmed, wata da aka ci zarafinta a wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar mijinta a kasarta Bangaladash, wadda duk da raunukan da ta samu yayin harin bata yi kasa a gwiwa wajen sanar da duniya sanadiyyar mutuwar mijin nata Avijit Roy ba.