Lakhdar Brahimi zai yi murabus | Siyasa | DW | 14.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Lakhdar Brahimi zai yi murabus

Babban jami'in diplomasiya da ke ƙokarin sulhunta rikicin ƙasar Siriya, Lakhdar Brahimi ya sanar da cewar zai sauka daga wannan muƙami a ƙarshen watan Mayu.

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce Brahimi ɗin ya dau wannan matakin ne saboda ƙasashen duniya sun gasa samun ci gaba a ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin basasa a Siriyan da aka kwashe shekaru 3 ana yi. Ɗan diplomasiyar dan ƙasar Algeria, ya daɗe yana tunanin yin murabus, amma sai a yanzu ne wakilin na Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar haɗin kan Larabawa, Lakhdar Brahimi ya tabbatar da cewar daga ranar 31 ga watan Mayu zai ajiye wannan nauyi da ke kansa. Sakatare-Janar na MDD, Ban Ki-moon ya ɗora laifin murabus ɗin na Brahimi a kan ƙasashen duniya waɗanda suka kasa daidaita kan rikicin Siriya. "Yana fuskantar gagGarumin aiki ne da ba zai iya shawo kansa ba. Ya yi namijin ƙoƙari, kuma ya nuna haƙuri da juriya kan aikin da ya tafiyar da ƙarfin zuciya, saboda ya san cewar al'ummar ƙasar, idan ba tare da yunƙurin samar da sabuwar Sririya ba, za su ci gaba da zama cikin kunci da wahala."

Syrien-Konferenz in Genf AUSSCHNITT & Symbolbild

Alamar rashin nasarar taron Geneva kan Siriya

Wani abin bakin ciki shi ne: shekaru uku tun bayan da 'yan tawaye suka tayar da yaƙi kan shugaban Siriya, Bashar al-Assad, har yanzu ba'a ga wata hanya ta kawo ƙarshen rikicin ba, wanda ya zuwa yanzu ya hallaka mutane aƙalla 150.000, wasu fiye da miliyan tara suka tsere daga yankunansu na asali.

Mawallafa: Antonija Böhm/Umaru Aliyu
Edita: Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin