Laberiya: Kotu ta dakatar da zagaye na biyu na zabe | BATUTUWA | DW | 01.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Laberiya: Kotu ta dakatar da zagaye na biyu na zabe

Zargin magudi a zagayen farko na zaben shugaban kasa ya sa kotun koli ba da umarnin haramta duk wasu shirye-shiryen gudanar da zagaye na biyu na zaben a ranar bakwai ga watan Nuwamba.

Kotun ta bukaci da a gabatar da dukannin koke-koken da ake da su kan zaben zuwa gobe Alhamis, inda za ta yi nazari kan kowane korafi da jam'iyyun suka mika. Babu dai tabbacin ko kotun za ta iya yanke hukunci kan sakamakon bincike kan irin zargi da ke gabanta 'yan kwanaki kalilan kafin gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar amma wannan mataki baya nufin ta soke zaben na ran 10 ga watan Octoba.

Libera, Charles Brumskine (picture-alliance/dpa/A.Jallanzo)

Dan takarar shugaban kasar Laberiya, Charles Brumskine

Charles Brumskine na jam'iyyar Librerty wanda ya zo na uku a zagaye na farko na zaben shi ya shigar da kara kan zargin tafka kura-kurai da suka sabawa doka. Tun farko dai jam’iyyar Unity Party mai mulki  da mataimakin shugaban kasa mai ci Joseph Boakai ya ke wa takara wanda kuma ya zo na biyu a zaben ta caccaki sakamakon farko na zabe. 

Sanarwar ta kuma zargi shugabar kasar mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf da yin shishigi a cikin harkokin zaben sakamakon wata ganawa da aka ce ta yi a gidanta da shugabannin hukumar zaben kasar tun ma kafin a je ga zagaye na farko, sai dai tuni shugaba Sirleaf ta karyata wannan zargi.

Georg Weah Liberia (picture-alliance / Pressefoto ULMER)

Dan takarar shugaban kasa a Laberiya, Georg Weah

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya George Weah mai shekaru 51 ya zo na daya da 39 cikin 100 na kuri’un da aka kada  wanda idan har kotun kolin kasar ta amince da sakamakon zaben, zai fafata da dan takaran jam’iyya mai mulki Joseph Boakai mai shekaru 72 wanda ya zo na biyu da kashi 29.1 cikin 100 a zagayen farko na zaben.

Tun dai kafin a je ga zagaye na farko na zaben, shugabar kasar mai barin gado ta yi kira ga 'yan kasar Laberiya da su su san daga inda suke kuma ina za su a kasar da ta fuskanci yakin basasa da ya hallaka al’ummar da yawanta ya kai dubu 250 daga 1989 zuwa shekara ta 2003 sannan ga matsalar annobar Ebola da ta biyo baya a 2016.

Sauti da bidiyo akan labarin