Laberiya: George Weah ya samu goyon baya | NRS-Import | DW | 26.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Laberiya: George Weah ya samu goyon baya

Daya daga cikin 'yan takarar neman shugabancin kasar Laberiya kuma tsohon madugun yakin basasan kasar Prince Johnson ya mara wa dan takara George Weah baya.

Tsohon madugun yakin mai shekaru 65 da haihuwa,  ya yi kira ga magoya bayansa da su zabi dan takara George Weah a zagaye na biyu na zaben da zai gudana a ranar bakwai ga watan Nuwamba mai zuwa.

Yayin zagayen farko na zaben da ya gudana na ran 10 ga wannan wata na Octoba, Sanata Johnson ya samu kashi 08,2 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada, yayin da dan takara  Weah ya zo na daya da kashi 38,4 cikin 100 a gaban abokin hamayyarsa kuma mataimakin shugabar kasar ta Laberiya Joseph Boakai  wanda ya samu kashi 28,8 cikin 100.

Sanata Prince Johnson ya ce ya yi wannan zabe ne inda yake ganin ya kyautu dukannin jam'iyyun adawa su marawa Weah baya domin a kayar da dan takarar jam'iyya mai mulki da boakai ke takara a karkashinta.