Rahotanni daga Monrovia fadar gwamnatin Laberiya na nunar da cewa yara 30 sun rasa rayukansu yayin gobara da ta tashi a wata makarantar allo.
Ofishin shugaban kasar Laberian George Weah ya bayyana cewa ya samu rahoton gobarar cikin dare daga hukumar bayar da agajin gaggawa. Tuni dai Shugaba George Weah ya kai ziyara makarantar da ke Paynesville a wajen birnin Monrovia tare da bayyana alhininsa. Wani mamba a kungiyar Fulani Amadou Sherrif ya nunar da cewa, gobarar ta tashi ne cikin dare a yayin da yaran ke bacci.