GAT
June 24, 2019Talla
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne ga gasar neman cin kofin kwallon kafar kasashen Afirka karo na 32 da ke gudana a kasar Masar inda a halin yanzu ake cikin buga wasannin zagayen farko na tankade da rairayen neman tikitin zuwa zagaye na biyu. Akwai kuma sauran gasannin da suka hada da ta cin kofin kwalon kafa ta mata ta duniya da ke gudana a Faransa da kuma ta 'yan kasa da shekaru 21 ta kasashen Turai a cikin shirin.