1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasannin 16.08.2021

August 16, 2021

Kungiyoyi da dama sun soma wasan sabuwar kakar wasannin kwallon kafar Turai da kafar dama a yayin da Novak Djokovic ya ci gaba da jan zarensa a gasar kwallon Tennis.

https://p.dw.com/p/3z3Ae
Fußball | Bundesliga | VfB Stuttgart - SpVgg Greuther Fürth | Jubel
Hoto: Thomas Niedermueller/Getty Images

Kungiyoyin VfB Stuttgart da Hoffenheim da Borussia Dortmund da Cologne da kuma Mainz sun fara kakar wasannin Bundesliga ta Jamus a bana da kafar dama, a karawar farko da aka yi ranar Jumma'ar makon da ya gabata tsakanin Bayern Munich mai rike da kambu da kuma ta lashe shi har sau tara a jere da Borussia Mönchengladbach sun tashi wasa kunne doki daya da daya. A karshen mako kuwa wasannin da aka fafata ranar Asabar, Kungiyar VfB Stuttgart ce ta yi wa kungiyar Fürth da ta hauro daga rukuni na biyu na Bundesliga mummunanr tarba da ci biyar da daya, yayin da ita ma Hoffenheim ta yi wa takwararta ta Augsburg dukan kawo wuka da ci hudu da babu.

Ita ma dai kungiyar kwallon kafa ta Wolfsburg, tarbar wasaraire ta yi wa kungiyar kwallon kafa ta Bochum da ita ma ta hauro sama daga Bundeliga rukuni na biyu a bana da ci daya mai ban haushi, yayin da aka tashi wasa tsakanin Arminia Bielefeld babu ci. Kungiyar Borussia Dortmund ta caskara Eintracht Frankfurt da ci biyar da biyu, wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Union Berlin da ta karbi bakuncin Bayer Leverkussen 04, an ta shi kunnen doki daya da daya.

A wasan da aka fafata ranar Lahadi kuwa, Mainz ta lallasa RB Leipzig da ci daya mai ban haushi, a wata nasara da za a iya cewa ta ban mamaki, kasancewar, 'yan wasan kungiyar da dama da kuma wasu jami'an kungiyar suka kamu da cutar annobar coronavirus da ta addabi duniya yayin da aka killace 'yan wasa 11 da kuma jami'an kungiyar uku sakamkon mu'amala da 'yan uwansu da suka kamu da cutar.

Za a iya cewa a bana Cologne ta fara kakar da kafar dama ba kamar bara ba, domin kuwa ta lallasa Herthe Berlin da ci uku da daya. A yanzu haka dai Stuttgat ce a saman tebur yayin da Hoffenheim ke bi mata a yawan kwallaye sai kuma Borussia Dortmund a matsayi na uku Cologne kuma na matsayin na hudu. Bayern kuwa na a matsayi na takwas ne, a yayin da Ausgburg da Fürth ke kasan tebur. 

Fitattun 'yan wasa da ma masu horas da 'yan wasa a Jamus, na ci gaba da mika ta'aziyyarsu dangane da rasuwar shahararren dan wasan kwallon kafa na Bayern Munich Gerd Mueller da kuma Jamus da ya rigamu gidan gaskiya yana da shekaru 75 a duniya.

Deutschland | Fußball Legende Gerd Müller ist tot
Marigayi Gerd MuellerHoto: Bikas Das/AP/picture alliance

A kasar Ingila, kungiyoyin Manchester United da Chelsea da West Ham da kuma Liverpool sun fara kakar ta bana da kafar dama. Dan wasan kwallon kafa na Liverpool din Muhammad Salah ya kafa tarihi, inda ya zura kwallo a wasan farko na kakar wasanni da kunyarsa ta samu nasara har sau biyar a jere. Shi ne dai dan wasa na farko da ya samu wannan nasara, baya ga Teddy Sheringham dan wasan Tottenham da Manchester United da shi ma ya zura kwallaye a wasanni hudu na farko a jere tsakanin shekarun 1992 zuwa 95.

A jiya Lahadi ne aka yi fafatawar karshe a gasar cin kofin kwallon Kwando ta jihohin arewacin Najeriya 19 a Kano, a filin wasa na Sani Abacha. Gasar dai ta fitar da kwararrun da za su shiga gasa ta kasa baki daya da za a gudanar a nan gaba.

A bangaren wasan kwallon Tennis kuwa, Novak Djokovic da ya lashe manyan gasa guda uku da aka gudanar a wannan shekara, ya sha alwashin sake lashe gasar da za a gudanar nan gaba ta US Open. Dan kasar Sabiya Djokovic ya kafa tarihin kwashe makonni 334 a matsayin dan wasan da ke sawun gaba, fiye da zakakuri Roger Federer da ya kwashe makonni 310 da a yanzu ke zaman na tara.