1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni

Mouhamadou Awal Balarabe
November 18, 2019

'Yan kasa da shekaru 17 da haihuwa na Brazil sun sake lashe kofin kwallon kafa na duniya a yayin da 'yan wasan Najeriya da kamaru suka yi abin yabo a wasanni neman tikitin shiga matakin karshe na gasar kwallon Afirka.

https://p.dw.com/p/3TFdP
EM Quali Deutschland Weißrussland
Hoto: Imago-Images/M. Müller

Brazil ta lashe Kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa bayan ta doke Mexico da ci 2-1 a wasan karshe da ya gudana a jiya Lahadi a birnin Gama da ke tsakiyar kasar. Dan wasa Lazaro wanda ya maye gurbi ne ya zura kwallo a mintunan karshe wanda ya sa Brazil cika burinta, kamar yadda ya faru a wasan kusa da na karshe da Faransa. Wannan dai shi ne karo na hudu da Brazil ta lashe kofin 'yan kasa da 17 ta duniya. Amma rabon kungiyar ta Brazil ta samu wannan bajinta tun 2003 shekaru 16 ke nan da suka gabata, ko da shi ke Brazil ta taba kasancewa zakaran duniya ta 'yan kasa da shekaru 17 a 1997 da 1999. Idan aka ce za a kalailaice ne ma dai, Brazil ta dauki fansa ne a kan Mexico wacce ta doke da ci 3-0 a wasan karshe na neman cin Kofin Duniya na U17 na 2005 da ya gudana a Peru. Baya ga Brazil a mtsayin farko Mexico na biya mata baya a matsayi na biyu, yayin da Faransa ta zo ta uku bayan da ta doke Holland da 3-1a wasan neman matsayi na kofin na duniya. 

Kasashe da dama sun cirewa kansu kitse daga wuta  An gudanar da wasanni rana ta biyu na neman cancantar shiga gasar kwallon kafa ta wannan nahiyar a shekarar 2021 kasar Kamaru. Kasashen da ake kira giwan kwalon kafa sun cire wa kansu kitse a wuta kama daga kamaru da Najeriya da Senegal.

U-17-Fußball-Weltmeisterschaft | Brasilien vs. Spanien
Hoto: Getty Images/AFP/M. Kiran

A rukunin farko Mali ta doke Chadi 2-0, lamarin da ke bai wa ita Mali damar jagorantar wannan rukunin A da maki hudu. Ita ma kungiyar Sily ta Guinea tana da maki hudu sakamakon lallasa Namibiya da ta yi da ci 2-0, kwallaye Issiaga Sylla da José Kanté ne suka sanya hannu. A rukuni na biyu kuwa, Burkina Faso ta samu nasara a kan Sudan 2-1, kuma ita Burkanina tana kankankan a yawan maki da Yuganda wacce ta ci Malawai 2-0. A rukunin na uku, Afirka ta Kudu ta ta yi wa Sudan ci mai ban haushi, nasarar da ya sa ta yi kunne doki da abokiyar hamayyarta da yawan maki. Ita ma Ghana tana fafatawa da Sao Tome da Principe a wannan Litinin. Yayin da rukuni na hudu Gabon ta doke Angola da ci 2-1 tare da daukar jagorancin rukunin har zuwa wasa tsakanin DR Kwango da Gambiya a yau.

Duk da cewa ta riga ta cancanta hayewa a matsayin mai daukar bakuncin gasar kwallon kofin Afirka, Kamaru ta barje gumi a wasanninta rukunin na biyar, inda kungiyar Indomitable Lions ta yi nasara a kan Rwanda a ci 1-0 kuma dukkanin kasashen biyu na da maki hur-hudu a biyau. Sai dai Mozambique da ke biya musu baya za ta kara da Cape Verde a wannan Litinin.

A rukunin na shida kuwa, Senegal ta gasa wa Eswatini wacce a da ake kira Swaziland aya a hannu a ci 4-1. Wannan Nasara ta biyu cikin wasanni biyu ya sa Senegal yi sauran kungiyoyin ratar maki uku. Yayin da Kwango-Brazzaville kuma ta doke Guinea-Bissau da ci 3-0. A rukuni na bakwai kuma na karshe kuwa, kwallo ta Jodel Dossou ya zura ya bai wa Benin damar doke Saliyo ci 1-0. Sai dai Super Eagles ta Najeriya da ke jan ragamar wannan rukuni ta samu nasara 4-2 a kan Lesotho.

Sai dai a ranar farko na wasan tankade da rairaye na kollon kafa na kasashen na afirka  ‘yan wasan mena na jamhuriyar Nijar ba su ji da dai ba domin takwarorinsu na Cote d’avoir sun dokesu da ci daya mai ban haushi a wasan da ya gudana na ranar Asabar a filin wasa na Felix Houphouet- Boigny da ke birnin Abija. Salissou Boukari ya halarci daya daga cikin wuraran da aka kalli wasan a birnin Yamai ga kuma rahoton da ya hada mana.

An fafata neman cancantar shiga gasar Euro 2020  A Turai kasashen nahiyar sun kara da juna don neman cancantar shiga gasar Euro a shekara ta 2020, kuma tuni kungiyar Mannschaft ta Jamus ta haye a ranar Asabar inda ta doke Belarus 4-0. Godiya ta tabbata ga Matthias Ginter, Leon Goretzka da Toni Kroos, wadanda suka zura kwallaye da suka taimaka wa Jamus lashe wasan kuma ta kare a matsayin farko a rukunin na uku a gaban Netherlands ko Holland. Amma duk da wannan cancantar, mai horas da Jamus Joachim Löw ya bayyana cewa kungiyarsa ba ta cikin rukunin wadanda za su iya taka rawar gani a gasar. Dama dai sanin kowa ne cewa tun bayan rashin abin arziki a gasar duniya ta Rasha, Mannschaft ta Jamus ba ta burge 'yan kallo da magoya baya duk da nasarar da takw samu. Ko da a ranar Asabar da ta gabta, magoya bayan 35,000 ne kawai suka kallon wasan Jamus a filin wasa na Borussia-Park a Mönchengladbach wanda ke daukar mutane 54,000. Ita ma Portugal da ke rike da kofin Turai a yanzu ta lashe tikitin shiga Euro 2020 ta hanyar doke Luxembourg da ci 2-0. Nasara ta samu ne daga kwallaye da Bruno Fernandes da Cristiano Ronaldo suka zuwa. hasali ma wannan shine kwallo na 99 a Ronaldo ya zira karkashin lemar Seleção ta Portugal. A wannan Litinin ne kungiyoyin na Turai za su i gaba da wasannin na neman cancanta, inda Switzerland da Denmark za su kece raini.

EM Quali Kroatien gegen die Slovakei
Hoto: Reuters/A. Bronic

A sauran fagen wasanni Wani dan Ruwanda Didier Munyaneza ya yi nasarar lashe tseren keke na kasa da kasa da ala saba shiryawa a kowace shekara a Senegal. Duk da cewa wannan shi ne tseren keke na 18 da aka shirya a kasar ta yammacin Afirka amma shi ne karon farko da matash Munyaneza nan Rwanda mai shekaru 21 da haihuwa ya ciri tuta a gasar keke a Afirka ta farko. Matakin tsere na bakwai kuma na karshe da ya gudana a jiya a birnin Dakar mai tsawon kilomita 106km, wani dan tseren keke na Thomas Lienert ne ya lashe shi. Amma nasarar da ba ta canza komai a sakamakon karshen ba kasancewar Didier Munyaneza ya riga ya yi musu ratar da ke da wuyan cikewa tun a mataki na biyu na tseren.

UK ATP Finals Kein erneuter Titel-Coup: Zverev verpasst Finale in London
Hoto: AFP/D. Leal-Olivas

A fagen tennis inda aka kammala Masters London da ke zama uwar gasanni ta shekara. dalili kuwa shi ne, gasar ta hada manyan 'yan wasa takwas na duniya, wacce a bana ta kare cikin nasarar Stefanos Tsitsipas. Shi dai dan kasar Girka mai shekaru 21 da haihuwa ya yi nasarar doke Dominic Thiem na Ostiriya da 6/7, 7/6, 6/2). Shi dai Tsitsipas ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya lashe kofin Master don London a tarihin gasar ta tennis.

A wani labarin kuma an soma sabon tsari na gasar Davis Cup a Madrid wadda za a shafe mako guda ana gudanarwa. Alahakika dai, kasashe 18 da aka kasa kashi 6 ne za su yi wasannin kalubale tsakaninsu a matakin farko. Wadanda za su samu hayewa ne a kowane rukuni, da kuma masu matsayi na biyu da ke da kyakkyawan sakamako ne, za su kara matakin karshe wanda zai fara daga wasan kusa da kusa da na karshe na 1/4.

Wannan sabon tsarin gasar tennis, wanda yayi kama da gasar cin kofin Duniya na kwallon kafa na ci gaba da shan suka daga wasu kasashe. Australiya da Faransa ga misali suna da matukar sukar wannan sabon zubin, wanda suke ganin cewa yana gurbata gasar kwallon tennis daya tilo da ake yinshi tsakanin kungiya zuwa kungiya. Sai dai wannan karo na 108 na Cup Davis zai samu halartar yawancin taurari tennis wadanda suka yi watsi da gasar a cikin 'yan shekarun da suka gabata ciki har da Novak Djokovic da Rafael Nadal.