Wasan lig na Jamus na Bundesliga na kara zafi
January 28, 2019A wasannin Bundesliga na karshen mako aka buga wasannin mako na 19 inda illahirin kungiyoyin da ke a sahun gaban tebirin na Bundesliga suka ci wasansu akasarinsu ma ci kaca inda alal misali Yaya Babba Bayern Münich ta lallasa Stuttgart da ci 4-1, Leipzig ta bi Dusseldorf har gida ta yi mata cin raba ni da yaro da ci 4 da nema, Mönchengladbach ta karbi bakuncin Augsburg ta kuma doke ta da ci 2 da babu, a yayin da Yaya Karama Borussia Dortmund wacce taurarinta ke ci gaba da haskawa ta karbi bakuncin Hannover a filin wasa na Signal Iduna Park a gaban 'yan kallo kusan dubu 80 ta wulakantata da ci biyar da daya.
A sauran wasannin Hertha Berlin ta tashi 2-2 da Schalke 04, Freiburg ta sha kashi a hannun Hoffenheim da ci 4-2, Mayence ta doke Nuremberg da ci 2-1, Lekerkusen ta lallasa Wolfsburg a gidanta da ci 3 da nema, a yayin da Bremen da Frankfurt suka yi kunnan doki da ci 2-2.
Har yanzu dai Kungiyar Dortmund ce a saman tebirinn na Bundesliga da maki 48, Bayern Münich na bi mata da maki 42, Mönchengladbach na a matsayin ta uku da maki 39 a yayin da Leipzig ke a matsayin ta hudu da maki 34.
Har yanzu dai muna kan batun kwallon kafar amma a wanann karo a nahiyar Asiya, inda aski ya kawo gaban goshi a gasar cin koffin kwallon kafa na nahiyar da ke gudana a Jamhuriyar Daular Larabawa. Tuni dai aka kori Koriya ta Kudu da Ostareliya mai rike da kofin, a yayin da kasashen Iran da Japan da Katar da Jamhuriyar Daular Larabawa suka kai zagayen kusa da na karshe.
Yanzu kuma sai wasan kwallon hannu inda a karshen mako aka kammala gasar cin kofin kwallon hannu ta duniya ta shekara ta 2019 da ta gudana a birnin Kolon na nan kasar Jamus. Kasar Danemark ce dai ta lshe kofin da ke zama karo na farko a tarihinta bayan da a wasan karshe ta doke kasar Norway da ci 31 da 22.
A fagen wasannin Tennis na Duniya inda a jiya lahadi aka kammala gasar farko ta wannan shekara ta Grand Chelem na kasar Ostareliya ko kuma Open d'Australie. inda a fagen maza dan kasar Sabiya Novac Djokovic ya lashe kofin bayan da ya doke Rafael Nadal na kasar Spain da ci 6-3,6-2,6-3. Kuma bayan kammala wasan Djokovic ya bayyana gamsuw.
A bangaren mata Naomi Osaka 'yar kasar Japan mai shekaru 21 ce ta lashe kofin gasar ta Open d'Australie bayan da ta doke Petra Kvitova 'yar Jamhuriyar Tchek da ci 7-6,7-2,5-7,6-4. Wannan ita ce babbar nasara ta biyu da Osaka ta samu a cikin watanni hudu baya ga kofin US Open da ta lashe a gaban Serena Williams.
Har yanz dai a bangaren maza Novac Djokovic ne ke a saman tebirin kwallon tennis na duniya, Rafael Nadal na a matsayin na biyu a yayin da Alexander Zverev dan kasar Jamus ke a matsayin na uku. A bangaren mata kuma Osaka wacce ke a matsayin ta uku kafin wannan gasa ta Open D'australie ta dare a halin yanzu tebirin na kwallon tennis a duniya, Kvitova na bi mata a matsayin ta biyu a yayin da Simona Halep 'yar Romaniya ke a matsayin ta uku.