1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin komawa wasannin Bundesliga

Suleiman Babayo GAT
January 14, 2019

A labarin wasannin za ku ji cewa a wannan mako ake komawa wasannin lig din kasar Jamus na Bundesliga bayan kammala hutun sabuwar shekara. Za mu kuma duba wasu fannonin wasannin.

https://p.dw.com/p/3BWA9
Deutschland Borussia Dortmund v Borussia Moenchengladbach - Bundesliga | Götze und Reus
Hoto: Getty Images/Bongarts/L. Baron

A wannan makon ake komawa wasannin lig na Jamus da ake kira Bundesliga, inda ranar Juma'a Hoffenheim da Bayern Munich za su kece raini, sai kuma ranar Asabar inda Stuttgart za ta fafata da Mainz, ita kuma Hannover da Werder Bremen, sai Frankfurt da Freiburg, sannan Leverkusen da Mönchengladbach yayin da Augsburg za ta karbi bakuncin Düsseldorf.

Zuwa lokacin da aka tafi hutun karshen shekara Borussia Dortmund ke jagorancin teburin na Bundesliga a Jamus da maki 42, yayin da Bayern Munich mai maki 36 ke matsayi na biyu, Mönchengladbach mai maki 33 tana matsayi na uku, yayin da Leipzig ke matsayi na huku da maki na 31, a matsayi na biyar akwai Wolfsburg mai maki 28.


A wasannin Premier Lig na Ingila da aka kara a kasrhen mako West Ham ta doke Arsenal 1 mai ban haushi, Chelsea ta doke Newcastle 2 da 1, yayin da Manchester United ta bi Tottenham ta doke ta 1 da nema. Ita kuma Everton ta samu galaba kan Bournemouth 2 da nema. Haka ita ma Burnley ta samu nasara kan FC Fulham 2 da 1.
Sannan da yammacin wannan Litinin ake kara wasa tsakanin Manchester City da Wolverhampton a wasannin na Premier League na Ingila.

England Fußball FC Liverpool Jürgen Klopp
Hoto: picture-alliance/ZumaPress/S. Calabrese


Idan muka tsallaka kasar Spain a wasannin La Liga da aka kara:
Rayo Vallecano 4, Celta Vigo 2
Leganes 1, Huesca 0
Valencia 1, Valladolid 1
Girona 1, Alaves 1
Villarreal 1, Getafe 2
Sunday's Matches
Atletico 1, Levante 0
Athletic Bilbao 2, Sevilla 0
Barcelona 3, Eibar 0
Betis 1, Madrid 2

Wannan sakamakaon ya nuna Lionel Messi dan kasar Ajentina wanda ya jefa kwallo na uku a mintoci 53 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ya zama dan wasa na farko da ya jefa kwallaye 400 a raga a wasannin La Liga na Spain. Luis Suarez dan kasar Uruguay ya jefa kwallaye biyu kafin ya taimaka wa Lionel Messi ya jefa nasa kwallon a raga. Duk 'yan wasan biyu sun fito daga yankin Latin Amirka.

La Liga - FC Barcelona vs Atletico Madrid Messi Tor
Hoto: Reuters/A. Gea


A wani abunda ke zaman kalubale ga kungiyoyin kwallon kafa na kasar Nijer, masu shawar wasanin sun fi maida hankali ga nuna shawarsu da ma goyon bayan manyan kungiyoyi na kasashen Turai a maimakon sun rungumi na cikin gida kamar yadda zaku ji a rahoton da wakilinmu na jihar tahoua Issoufou Mamane ya aiko muna:


A fage wasan Tennis an fitar da jerin gwanayen wasan na wannan shekara, inda yanzu haka Novak Djokovic dan Sabiya ke matsayi na farko, a gaban Rafael Nadal wanda ya fi shahara dan kasar Spain da yanzu haka ya koma matsayi na biyu, kana Roger Federer dan kasar Switzerland yana matsayi na uku.
Tuni aka fara zagaye na farko na daya daga cikin gasar wasannin mai tasiri da ake kira Australian Open, wanda yake gudana a birnin Melbourne. Akwai 'yan wasa da dama da suke ciki, inda aka fara tankade da reraya zuwa lokcin da za a samu zakara a gasar mai tasiri ta farko a shekara, sannan a ci gaba har zuwa sauran manyan gasar hudu da suke da muhimmanci, inda kowace shekara ake yin guda biyar, kuma dama Australian Open ke zama a farko duk shekara.

ATP Finals Novak Djokovic gewinnt gegen Kevin Anderson
Hoto: Reuters/A. Couldridge