1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Yadda ta kaya a karshen mako

Suleiman Babayo LMJ
February 26, 2024

Yanda ta kaya a wasu daga cikin wasannin lig na kasashen Turai, kana kasar Ghana ta kammala shirin karbar bakuncin wasannin kasashen Afirka da ma wasu fannonin wasanni.

https://p.dw.com/p/4ctZM
Ingila | London | Crystal Palace | Magoya Baya
Magoya bayan kungiyar Crystal Palace, na nuna adawarsu da aikata laifuka da wukakeHoto: Katie Chan/Action Plus/picture alliance

Ba mu fara da Premier League ta kasar Ingilan, inda sakamakon wasannin karshen makon suka kasance kamar haka:

Crystal Palace 3,          Burnley 0

Man United 1,              Fulham 2

Bournemouth 0,           Man City 1

Arsenal 4,                   Newcastle 1

Wolverhampton 1,       Sheffield United 0
A wasannin lig na Faransa kuwa ga yadda sakamakon yake:

Farasan | PSG |  Achraf Hakimi
Achraf Hakimi na kungiyar kwallon kafa ta PSG ta Faransa na gara kwalloHoto: Julien Mattia/Le Pictorium/dpa/picture alliance

PSG 1,                  Rennes 1

Metz 1,                Lyon 2

Lorient 0,             Nantes 1

Strasbourg 0,        Brest 3

Lens 2,                 Monaco 3

Toulouse 3,          Lille 1

Nice 0,                 Clermont Foot 0

Le Havre 1,           Reims 2

Bundesliga | Borussia Dortmund | TSG Hoffenheim
Borussia Dortmund ta yi abin kunya a gidaHoto: Ina Fassbender/AFP/Getty Images

Sannan a Jamus a wasannin Bundesliga da aka kara, Borussia Dortmund ta sha kaye a gida a hannun Hoffenheim yayin da Bayern Munich ta samu nasara a gida a karawarsu da RB Leipzig. Ita ma Leverkusen da ke saman tebur ta samu nasara a gida a wasanta da Mainz, abin da ya sanya ta ci gaba da trike kambunta. Ga dai yadda sakamakon wasannin ya kasance:

Leverkusen 2,              Mainz 1

Union Berlin 2,             Heidenheim 2

Monchengladbach 5,   Bochum 2

Bremen 1,                   Darmstadt 1

Bayern Munich 2,        RB Leipzig 1

Eintracht 2,                 Wolfsburg 2

Dortmund 2,               Hoffenheim 3

Stuttgart,                     Cologne 1
A karshen bayan zanga-zanga daga magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa da ke kara wasan lig na Jamus na Bundesliga, Hukumar Kula da Wasannin Lig din DFL ta dakatar da matakin shigar da ma su zuba jari domin samun kudin da ake bukata a wasannin na Bundesliga. Akwai kungiyoyi 36 da ke kara wasannin na Bundesliga, a mataki na farko da na biyu. Tun da fari hukumar ta nemi sayar da nuna wasannin ga kafofin yada labarai, abin da ya janyo zanga-zangar tsayar da wasanni da dama a matakan biyu na Bundesliga daga magoya bayan kungiyoyi. Matakin magoya bayan dai a yanzu ya tilasta wa Hukumar Kula da Wasannin Lig-Lig ta Jamus din, soke wannan kuduri nata na amincewa da zuba jari a wasannin na Bundesliga.

Bundesliga | Zanga-Zanga | DFL | Zuba Jari
Magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa na Bundesliga sun cimma nasara a kan DFLHoto: Frank Hoermann/Sven Simon/IMAGO
Jamus | Toni Kroos | Manschaft
Toni Kroos zai dawo bugawa kungiyar kwallon kafar Jamus ta ManschaftHoto: Marvin Ibo Güngör/GES/picture alliance

Bayan shafe tsowon lokaci ana yada jita-jita a karshe ta tabbata cewa Toni Kroos zai sake dawowa cikin tawaogar 'yan wasan kwallo kafa na Jamus lokacin bazara da ke tafe, a yayin gasar neman cin kofin kasashen Turai. Dan wasan mai shekaru 34 da haihuwa wanda yake cikin tawagar Jamsu da ta lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2014, ya tabbatar da wannan dawowa a shafinsa na sada zumunta. Ya fice daga cikin tawagar 'yan wasan Jamus ne, tun bayan wasan cin kofin kwallon kafa na kasashen Turai a shekara ta 2020.