1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi ruwan kwallaye a mako na 23 na Bundesliga

Mouhamadou Awal Balarabe AH
March 1, 2021

Sa'o'i 24 kacal suka rage wa kotun da ke sauraren kararrakin wasanni ta yanke hukunci kan karar da shugaban CAF Ahmad Ahma ya shigar bayan da FIFA ta dakatar da shi na tsawon shekaru biyar.

https://p.dw.com/p/3q3LT
Afrika Fußball Ahmad Ahmad
Hoto: FADEL SENNA/AFP via Getty Images

 Idan kotun ta wanke shi, shi dan Madagasakar din zai iya kokarin neman wa'adi na biyu a zaben shugabancin hukumar kwallon kafa ta kasashen Afirka da zai gudana a ranar 12 ga watan Maris a kasar Maroko. Wannan zai iya zama dama ta dawo wa CAF da martabarta a idanun duniya sakamakon shisshigi da FIFFA da Shugabanta Infantino suke a harkokinta.Tun bayan kayar da Issa Hayatou a CAF, aka dora fata a kan Ahmad Ahmad don ya ciyar da kwallon kafa a Afirka gaba, amma maimakon haka, cin hanci da karbar rashawa ya samun gindin zama, Steven Lavon, dan jaridar wasanni na Togo. “Cin hanci da rashawa ya ci gaba. Gaskiya ne cewa an yi gyare-gyare da yawa don a sami damar dakatar da irin wannan dabi'ar. Amma yana da matukar wahala a juya babin cin hanci da rashawa cikin dare daya. "Yayin da makomar Ahmad Ahmad ta kasance a hannun kotu, ‘yan takara hudu ne ke zawarcin shugabancin hukumar CAF, ciki har da Attajirin nan dan Afirka ta Kudu Patrice Motsepe, da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Cote d' Ivoire Jacques Anouma. Sauran 'yan takara biyu sun hada da  Ahmed Yahya na Moritaniya da Augustin Senghor na Senegal. 

Kungiyar Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu ta yi wa takwararta ta Belouizdad ta Aljeriya dukan kawo wuka 

FIFA U 20 Fußball WM 2019 Achtelfinale Senegal - Nigeria
Hoto: Imago Images/Newspix/L. Sobala

Mako guda bayan dage wasan neman lashe kofin kwallon kafa na kungiyoyin Afirka da ke rike da bajintar zakara na kasashensu sakamon yaduwar annobar corona, Kungiyar Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu ta yi wa takwararta ta Belouizdad ta Aljeriya dukan kawo wuka 5-1, a filin wasa na birnin Dar Es Salam na kasar Tanzaniya. Wannan nasarar ta bai wa zakaran Afirka ta Kudu damar darewa saman teburin rukuni na biyu na Champions League din Afirka, saboda a wasanta na farko na rukuni-rukuni ta fara doke Al Hilal da ci 2-0, lamarin da ya sa Mamelodi samun jimillar maki shida a wasanni biyu, yayin da Tout Puissant mazemba ta Kwango dimukaradiyya ke biya mata baya da maki biyu. A daya wasan da ya gudana a rukuni na hudu a karshen makon kuwa, Wydad Casablanca ta Maroko ke jagorantar rukunin a halin yanzu sakamakon cin kaca da ta yi wa Kaizer Chiefs ta Afirka ta Kudu da ci 4-0. Shi ma wannan wasan da ya kamata ya gudana tun makonni biyun da suka wace a Tunisiya, an dage shi bisa dalilai na corona kuma ya gudana a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso. Har yanzu dai muna nahiyar Afirka, inda tafiya ta yi nisa a kokarin neman lashe kofin kwallon kafa na 'yan kasa da 20 da haihuwa a Kasar Moriteniya. Tunisiya da Yuganda za su kece raini da dare don neman tikitin kai wa wasan karshe, yayin da Ghana za ta fara wasa da Gambiya. Sau uku ne Ghana ta taba lashe gasar 'yan kasa da 20 da haihuwa, kuma yanzu magoya bayan 'yan kasa da 20 na Ghana suka nuna gamsuwa dangane da yadda 'yan wasansu suka taka leda da rawar da dan wasansu na tsakiya ya take.

An yi ruwan kwallaye a mako na 23 na Bundesliga

Fußball Bundesliga 23. Spieltag | Bayer Leverkusen vs. SC Freiburg | 2. TOR Freiburg
Hoto: Lars Baron/Getty Images

A nan Jamus kuwa, a karshen wannan makon ne aka gudanar da wasannin mako na 23 a gasar Bundesliga na kakar bana. Kuma mako guda bayan rashin nasarar a kan Eintracht Frankfurt, Yaya babba Bayern Munich ta murmure sosai kuma ta huce haushinta a kan Cologne da ci 5-1 a gida Allianz Arena. Godiya ta tabbata ga dan kwallon Kamarun nan Eric Maxim Choupo-Moting wanda ya zura daya daga cikin kwallayen, da ke zama na farko a gare shi tun bayan da aka soyo shi daga paris Saint Germain na Faransa. Wannan kyakkyawar nasarar ta bai wa Bayern Munich damar  kasancewa a saman tebur da maki 52 kuma tana sama da dukka tana ci gaba da samu ratar maki biyu kacal a gaban RB Leipzig wacce ke da maki 50 a halin yanzu. Maki biyu Ita RB Leipzig da Julian Nagelsmann ke horaswa ta fi gamsarwa a nasarar da ta samu fiye da yaya babba, saboda lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci, Borussia Mönchengladbach na bin ta kwallaye biyu, amma Leipzig ta yi ta gwagwarmaya har zuwa karshen wasan don farkawa tare da doke takwaratata da ci 3-2 a dakikonkin karshen lokaci bisa kokarin Alexander Sorloth da ya ci kwallon karshe. Dan wasan gaba Yussuf Poulsen na RB Leipzig ya yaba karfin halin da abokan karawarsa suka nuna:"Wannan nasara ce da muka cancanta. Mun yi rawar gani. Ba damuwa ne fara bin mu kwallaye biyu da aka yi, saboda mu iya mayar da martanin da ya dace. Yarda da kai na da matikar muhimmaci a lokacin da kuka samu kanku a irin wannan hali. Mönchengladbach dai tawaga ce mai kyau, amma mun yi nasarar doke su, a bayyane yake cewa mun fi su bajinta a filin wasa."A wannan karon ma dai Wolfsburg ta bada damar kafa murhu a matsayi na uku da maki 45 bayan da doke Hertha Berlin da ci 2-0, ciki har da kwallon da matashin dan Faransa mai tsaron baya Maxence Lacroix ya zura, mai shekara 20 da haihuwa. Wannan shi ne wasa na 9 da tare da an doke Wolfsburg a jere ba, wacce za ta kara da RB Leipzig a daren Laraba a wasan dab da na kusa da karshe na Kofin Jamus. A matsayi na hudu na Bundesliga kuwa, har yanzu dai Eintracht Frankfurt ce, duk da duka da ta sha a hannun Werder Bremen da ci 2-1. Sai dai a daura da haka, Yaya karama Borussia Dortmund ta lashe wasa na biyu a jere, inda ta yi kaca-kaca da Bielefeld 3-0, lamarin da ya sa ta rage maki uku tsakaninza da Frankfurt. A gefen babban abokiyar hamayyar Dortmund kuwa,  wato Schalke 04, laya ba ta yi kyan rufi ba saboda ta fadi kasa warwas a gaban VfB Stuttgart da ta doke ta da 5-1. Wannan rashin nasara na 16 na kakar bana ta dada jefa Schalke a sahun 'yan baya ga dangi. 

Premier League: Chelsea da Manchester ba su burge ba a wasannninsu

Fußball England Manchester City Ilkay Gündogan
Hoto: Laurence Griffiths/PA/dpa/picture alliance

A Premier League din Ingila kuwa, mabu wanda ya sami nasara a karon batta da aka yi a mako na 26 tsakanin Chelsea da Manchester United inda aka tashi (0-0). Kungiyoyin biyu da ake ji da su a fagen tamaula ba su burge ba a wasan, amma maki guda da ta samu ya sa ta kasance a matsayi na biyu a teburin lig din da maki 50 kuma a gaban Leicester mai maki 49 a matsayi na uku bayan da ta doke Arsenal da ci 3-1. Ita kuwa Liverpool ta doke kurara baya Sheffield (2-0). Amma kuma  Manchester City na fadada tazarar ta bayan doke West Ham a ranar Asabar (2-1), lamarin da ya sa ta samun nasara 14 a jere kuma take jagorancin lig din da maki 62. Ana sa ran cewar wasan da za a buga tsakanin kungiyoyin biyu na Manchester a ranar Lahadi 7 ga Maris, watakila ya zama dama ta karshe ga United na hana abokiyar hamayyarta ta City neman samun bajintar zakara a karo na bakwai.