1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: An bai wa Marco Rose jan kati

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
December 6, 2021

An bai wa mai horas da 'yan wasan Dortmund Marco Rose katin kora a yayin da CAF ta haramtawa Super Eagles na Najeriya buga wasa a filin kwallon kafar mallakarsu da ke Lagos.

https://p.dw.com/p/43u1f
Fußball Bundesliga Union Berlin  - Borussia Mönchengladbach
Hoto: POOL/AFP via Getty Images

Hukumar CAF ta haramtawa 'yan wasan Najeriya buga wasanninsu na gida a filin kwallon kafar mallakarsu da ke Lagos. Bayern Munich ta lallasa abokiyar hamayyarta Borussia Dortmund. Ga dukkan alamu sabon mai horas da 'yan wasan Manchester United ya fara da kafar dama.

A karshen mako a kakar wasannin Bundesliga ta bana a Jamus, a ranar Jumma'ar da ta gabata kungiyar kwallon kafa ta Union Berlin ta RB Leipzig da a bana kwallon ta zo mata a bai-bai da ci biyu da daya kana a ranar Asabar VfL Bochum ta bi Augsburg har gida ta kuma lallasa ta da ci uku da biyu kana aka tashi kunnen doki daya da daya a tsakanin FC Cologne da Arminia Bielefeld. Sai kuma wasan da ya fi daukar hankali wato na manyan giwaye Borussia Dortmund da Bayern Munich da ta kai mata ziyara, inda Bayern din ta bi Dortmund har gida ta kuma caskara ta da ci uku da biyu.

Fußball I Borussia Dortmund vs Bayern München
Bayern Munich ta lallasa Dortmund Hoto: Martin Meissner/AP/picture alliance

An dai buga wasa biyu da biyu, kafin daga bisani Bayern din ta samu kwallo na uku a wani bugun daga kai sai mai tsaron gida da ta samu, bayan dan wasan baya na Dortmund ya taba kwallo da hannunsa a yadi na 18. Sai dai ba wai a bugun daga kai sai mai tsaron gidan abin ya tsaya ba, domin kuwa an bai wa mai horas da 'yan wasan Dortmund din Marco Rose katin kora wato jan kati.

A wasan da aka fafata tsakanin Leverkussen da Greuther Fürth, inda Leverkussen tai wa Fürth dukan kawo wuka da ci bakwai da daya kana Mainz ta lallasa Wolfsburg da ci uku da nema. Ita kuwa Hoffenheim ta lallasa Eintracht Frankfurt ne da ta kai mata ziyar da ci uku da biyu. A wasannin da aka kara a ranar Lahadin da ta gabata kuwa, an tashi wasa canjaras ci biyu da biyu a wasan da aka fatata tsakanin Stuttgart da Herthe Berlin, hakan Freiburg ta bi Borussia Mönchengladbach har gida ta kuma casa ta da ci shida da nema. Kungiyar Bayern Munich dai ta ci gaba da rike matsayinta na saman tebur da maki 34 yayin da Borussia Dortmund ke biye mata a matsayi na biyu da maki 30 sai kuma Leverkusen a matsayi na uku da maki 27.

Fußballtrainer Ralf Rangnick
Ralf Rangnick sabon kocin Manchester UnitedHoto: Frank Hoermann/SVEN SIMON/picture alliance

Idan muka leka gasar Premier League ta Ingila kuwa ana iya cewa sabon mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ralf Rangnick ya fara da kafar dama, bayan da United din ta samu nasara a wasan da suka fafata da Crystal Palace da ci daya mai ban haushi. Kana ita ma Liverpool  ta sha da kyar da ci daya mai ban haushi a wasan da suka fafata da Wolverhampton.  Manchester City ta caskara Watford FC da ci uku da daya kana Chelsea ta sha kashi a hannun West Ham da ci uku da biyu. A yanzu haka dai, Manchester City ta kwace kambun saman tebur daga Chelsea da maki 35 yayin da Liverpool ke matsayi na biyu da maki 34 sai kuma Chelsea a matsayi na uku da maki 33.

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afrika ta sanar da haramtawa 'yan wasan kungiyar kwallon kafan Najeriya Super Eagles, yin amfani da filin wasa na Teslim Balogun da ke Lagos domin gudanar da duk wani wasan kasa da kasa saboda rashin kyau da ingancin filin. 

Tennis I Davis Cup Finale I Andrey Rublev
Andrey Rublev na kasar RashaHoto: Manu Fernandez/AP/picture alliance

Kasashen Birtaniya da Sabiya sun samu tikitin zuwa gasar kwallon Tennis ta duniya Davis Cup ta shekara mai zuwa. Kasashen biyu dai tare da Croatia da Rasha da suka samu nasarar kai wa ga wasan karshe a gasar ta bana, sujn samu wannan damar ne bayan da Sabiya ta sha kashi a hannun Croatia a wasan kusa da na karshe kana Birtaniya ta kuma kwasar kashinta a hannun Jamus. Akwai yiwuwar Rasha ta lashe kofin na gasar Tennis ta duniya na Davis Cup a karo na uku, bayan da dan wasanta Andrey Rublev ya lallasa takwaranasa na Croatia Borna Gojo da ci 6-4 da 7-6, abin da ya sanya suke da nasara ta ci daya da nema.

Akwai yiwuwar ba za a san zakaran gasar tseren motoci ta bana ba sai a makon karshe, ganin yadda tun daga farkon gasar ake tafiya kan-kan-kan a tsakanin zakaran da ke rike da kambun Lewis Hamilton da kuma Max Verstappen. Wannan dambarwa dai ta sanya gasar ta bana bayar da mamaki. Abin tambayar a nan shi ne, shin za'a samu sabon zakaran tseren motoci ne ko kuma Hamilton zai ci gaba da rike kambunsa?