1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon gasar kwallon kafa da tennis

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
September 19, 2022

Bayern Munich ta rikito zuwa mataki na biyar a kan teburin kakar Bundesliga a yayin da aka kammala gasar tennis ta US Open ba tare da kwararren dan wasan nan Novak Djokovic ba.

https://p.dw.com/p/4H44u
Bundesliga Dortmund Schalke Moukoko Tor
Hoto: David Inderlied/dpa/picture alliance

Kasar Kanada ta samu damar halartar gasar a karo na biyu, wadda za a fatata a kasar Qatar a karshen wannan shekara ta 2022 da muke ciki, Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta amince mata da ta dauki nauyin gasar ta 2026 da hadin gwiwar kasar Mexico. A yanzu haka ana ci gaba da shirye-shiryen halartar gasar cin kofin kwallon kafar ta duniya da kasar Qatar ke karbar bakunci, koda yake wasu kasashe kamar Jamus na nuna fargaba dangane da batun take hakkin dan Adam da ake zargin mahukuntan na Doha da aikatawa.

Bundesliga | 1. FC Union Berlin - VfL Wolfsburg
Hoto: JOHN MACDOUGALL/AFP/Getty Images

Kamar yadda kuka ji tun da farko, kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta sha kaye a makon da ya gabata da ci daya mai ban haushi a hannu kungiyar kwallon kafa ta Augsburg a fafatawar da suka yi a Asabar din karshen mako. Tun da fari dai a fafatawa ta farko da aka yi mako na bakwai na wasannin Bundesligar, an tashi wasa kunnen doki daya da daya tsakanin Mainz da Hertha Berlin.

A sauran wasannin da aka fafata a Asabar din karshen makon kuwa, Stuttgart ta sha kashi a hannun Frankfurt da ci uku da daya kana Borussia Mönchengladbach ta lallasa Leipzig da ci uku da nema. An tashi wasa kunnen doki daya da daya tsakanin Bayer Leverkussen da Werder Bremen kana Borussia Dortmund ta lallasa Schalke 04 da ci daya mai ban haushi.

A ranar Lahadin da ta gabata, kuwa an tashi wasa kunne doki daya da daya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Bochum da Cologne, an kuma tashi wasa canjaras babu ci tsakanin Hoffenheim da Freiburg kana Union Berlin ta lallasa Wolfsburg da ci biyu da nema. Wannan nasara ce ma ta bai wa Union Berlin din damar ci gaba da zama daram a saman teburin Bundesliga a bana da maki 17, inda Borrussia Dortmund ke biye mata a matsayi na biyu da maki 15 sai kuma Freiburg a matsayi na uku da maki 14.

Fussball Champions League FC Barcelona, Barca 09
Hoto: IMAGO/Eibner

A La ligar kasar Spain kuwa, Barcelona ta lallasa Elche da ci uku da nema, kana ita ma Valencia ta lallasa Celta de Vigo da ci uku da nema yayin da Real Madrid ta caskara Atletico Madrid da ci biyu da daya duka a mako na shida na gasar La liga ta bana. A yanzu dai Real Madrid ce a saman tebur da maki 18 yayin da Barcelona ke biye mata da maki 16 sai kuma Real Betis Bolompie a matsayi na uku da maki 15.

Fußball Europa League | Logo KAA Gent - Tottenham Hotspur | Logo Gent
Hoto: picture-alliance/dpa/Belga/J. Jacobs

A gasar Premier League ta Ingila kuwa, kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta yi ruwan kwallaye a ragar Leicester City, inda ta caskara ta da ci shida da biyu. An tashi wasa tsakanin Newcastle United da Bournemouth kunnen doki, kana Manchester City ta lallasa Wolverhamton Wanderers da ci uku da nema. Everton ta lallasa West Ham United da ci daya mai ban haushi, an kuma dage wasannin tsakanin Manchester United da Leeds da kuma wasa tsakanin Chelsea da Leverpool. Ita ma dai Arsenal ta lallasa Brentford da ci uku da nema, abin da ya sanya ta ci gaba da rike kambunta na saman tebur da maki 18 bayan wasanni takwas. Yayin da Manchester City da Tottenham ke biye mata a matsayi na biyu da na uku da maki 17 kowaccensu.