Labarin Wasanni 19:08:2019 | Zamantakewa | DW | 19.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Labarin Wasanni 19:08:2019

Bayan da ta doke kungiyar Augsburg da ci biyar da daya a wasan farko na kakar wasannin Bundesliga ta wannan shekara ta 2019-2020, kungiyar Dortmund ta dare saman tebirin Bundesliga.

Saurari sauti 09:55

A wasannin farko na gasar Bundesliga ta shekarar bana, kungiyar Dortmund wacce ta doke ta Augsburg da ci biyar da daya ta dare a saman tebirin Bundesliga da maki uku. Kungiyar leipzig wacce ta lallasa Union Berlin da ci hudu da babu na a matsayin ta biyu da maki uku a yayin da Freiburg wacce ta casa Mainz da ci uku da nema na a matsayin ta uku. Bayern Münich wacce ta yi kunnan doki 2-2 da Hertha Berlin na a matsayin ta bakwai a halin yanzu.

A ci gaban kasuwar cinikin 'yan wasa, kungiyar Bayern Münich ta aro shahararren dan wasan Brazil mai buga wa Barcelona wasa Philippe Coutinho. Kudin aron dan wasan wanda zai buga wa Bayern Münich wasa a tsawon shekara daya sun tashi miliyan takwas da rabi na Euro.

A sauran labaran kuma muna tafe da gasar tseren kafa da ta cin kofin kwallon kondo da dai sauransu.