1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin wasannin karshen mako

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
October 18, 2022

Yadda ta kaya a wasannin hamayya a manyan lig na kasashen Turai da kuma sakamakon wasannin share fage na gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka.

https://p.dw.com/p/4IHXH
Dan wasan Kungiyar PSG
Neymar na kasar BrazilHoto: JBAutissier/Panoramic/IMAGO

An gudanar da zagaye na biyu na wasannin share fage na gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka ta wato Confederation cup, yanzu an san wadanda suka haye matakin rukuni na gasar zakarun Afirka. A daya bangaren kuma, an gudanar da wasannin hamayya a manyan Liga na kasashen Turai, inda Real Madrid ta doke FC Barcelona a La Liga na Sipaniya.

Zakaran kwallon kafar Yuganda Vipers SC ta taka rawar gani a Lubumbashi, inda ta lallasa TP Mazembe da ta taba lashe kofin zakarun Afirka sau biyar da ci 4-2 a bugun fenareti, wanda hakan ya sa ta samu tikitin shiga matakin rukuni na cin kofin zakarun Afirka a karon farko a tarihinta. Ita ma Al Ahly ta Masar da ke zama daya daga cikin giwayen nahiyar, ita ma ta tsallake bayan da ta lallasa Kungiyar Monastir ta Tunisiya da ci 3-0. Kazalika Esperance ta Tunisiya da gumin goshi ta yi nasarar yin waje road da Plateau United sakamakon kwallon da ta zura a waje duk da ta sha kashi a wasan farko da ci 2-1. Ita kuwa Raja Club Athletic ta samu gurbin ne bayan ta lallasa Nigelec ta Nijar da ci 3-0 a jimllance, bayan da suka tashi 1-0 a karawarsu ta biyu a Casablanca.

Kungiyar Al-Ahly
Yan wasan Kungiyar Al-Ahly Hoto: Karim Jaafar/AFP/Getty Images

Kungiyar Al Merrikh da ke wakiltar Sudan ita ma ta samu tikitin shiga wasan rukunin cin kofin zakaraun Afirka sakamakon kwallon da ta ci a waje, duk da rashin nasara a hannun Ahli Tripoli na Libya da ci 3-1 a karshen mako. A daya wasan kuma, JS Kabylie ta Aljeriya ta samu gurbi a matakin rukuni da jimillar kwallaye 3-2 bayan doke AS Kara ta Togo. Sauran kungiyoyin kasashen Afirka da suka haye sun hada da Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu Petro Luanda ta Angola da Zamalek ta Misira sai kuma CR Belouizdad ta Algeriya.

Kungiyoyin da ke taka leda a gasar cin kofin confederation cup na Afirka sun kammala zagaye na biyu na share fagen gasar a karshen mako. A cikin mummunan yanayi, Renaissance Sportive de Berkane ta Moroko ta  cancanci yabo bayan da ta mamaye Kwara United ta Najeriya duk da rashin nasara da ci 1-3 a wasan farko. Hasali ma duk sauran manyan kungiyoyin sun kai labari, ciki har da Pyramids ta Masar da ta ci Hilal Alsahil ta Sudan da ci 7-0 a yayin da Azam ta Tanzaniya ta doke Al Akhdar ta Libiya da ci 2-0. Su ma Diables Noirs daga Kwango Brazaville da Motema Pembe daga Jamhuriyar Dimokradiyya Kwango sun samu nasara cikin sauki.

Fafatawar Madrid da Barcelona
Fafatawar Madrid da BarcelonaHoto: Manu Fernandez/AP/picture alliance

Kungiyar Real Madrid ta kama hanyar zama gagara-ba-dau a lig din kwallon kafar Sipaniya bayan da ta buga wasanta na tara ba tare da an doke ta ko da sau daya a bana ba. Alal-hakika ma dai ta yi nasarar lallasa abokiyar gabarta Barcelona da ci 3-1 a lamarin da ke zama farau da aka doke Barca a kakar wasa ta bana. Wannan nasarar ta bai wa Real damar darewa saman teburin lig din Sipaniya tare da yi wa Barcelona ratar maki uku.

Kazalika, daya daga cikin 'yan takarar Ballon d' Or wato Karim Benzema ya taka rawar gani a wasan a daidai lokacin da ake shirin bayyana gwarzon dan kwallon kafar duniya da ya lashe kyautar Ballon d'Or a wannan Litinin 17 ga watan Oktoba. Hasali ma dai, baya ga lashe La Liga da ya yi a bara da Champions League, Karim Benzema mai shekaru 34 na kan gaba a cin kwallaye a La Liga ta Sipaniya da ma zakarun Tura.

Kasancewar El-Classico ya zama mafi shahara cikin wasannin kwallon kafa a duniya, ya sa ma'abota kwallon kafa da magoya bayan kungiyoyin Real Madrid da Barcelona, sun sadaukar da lokacinsu wajen kallon yadda wadannan manyan giwaye za su kece rai ni a tsakaninsu. 

A Faransa ma dai,  an yi wasan na hamayya a mako na 11 a gasar Ligue 1, inda Paris St Germain ta yi nasara a kan Olympic Marseille da ci 1-0. Dan wasanta na gaba Neymar ne ya ci  daya-dayan kwallon a minti na 45, wanda kuma ke zama kwallo na 200 da ya ci tun bayan da ya rungumi kwallo a matsayin sana'a.

Kylian Mbappe na PSG
Kylian Mbappe na PSGHoto: Michel Spingler/AP Photo/picture alliance

Marseille ta samu muhimmiyar damar farke kwallon da ake bin ta, amma jan katin da aka ba wa dan wasanta Samuel Gigot  ya jawo mata koma baya. Yayin da PSG ke ci gaba da kasancewa a saman teburi bayan da ta ci wasanta na tara da canjaras biyu a makonni 11, a daidai lokacin da zakakurin dan wasanta Kylian Mbappe ya karyata rada-raden da ake yayatawa cewar zai bar Paris St Germain a watan Janairu, inda ya ce, bai fada ba.

A Premier Lig kuwa, Manchester City ta baras da wasanta na farko a mako na 11 na gasar Premier, inda Liverpool ta casa ta da ci 1-0, lamarin da ya bai wa Arsenal dama ta doke Leeds (1-0) damar jagorantar babban lig din Ingila. Ita kuwa Manchester United ta tashi 0-0 a wasan da ta yi da Old Trafford. Yayin da mai horas da Newcastle United ya kawar da duk wata shawarar siyan Cristiano Ronaldo don buga musu kwallo. Eddie Howe ya ce, shekarun dan wasan gaba na Manchester United dan asalin Portugal Ronaldo sun fara ja.

Yanzu kuma sai mu zo gida Jamus, inda a makon na 10 na gasar Bundesliga, Bayern Munich da Union Berlin suka kara. Ita Union Berlin da ke daukar bakuncin wasan ta lallasa Borussia Dortmund 2-0. Kuma ma ba wai fitattun 'yan wasan irin su Sheraldo Becker ko Jordan Siebatcheu ne suka zira kwallaye ba, amma dan wasan tsakiya Jannik Haberer ne ya ci dukan kwallayen biyu, lamarin da ya ba wa Union Berlin damar karfafa matsayinta na jagoran Bundesliga da maki 23.

Union Berlin na saman teburin Bundesliga
Union Berlin na mataki na daya a BundesligaHoto: O.Behrendt/IMAGO

A yanzu dai Union Berlin ta yi wa Bayern Munich da ke a matsayi na biyu zarrar maki hudu. Ita kuwa Freiburg ta koma a matsayi na uku, yayin da Hoffenheim da ta yi nasara da ci 3-0 a kan Schalke 04 da Eintracht Frankfurt wacce ta doke Bayern Leverkusen da ci 5-1 suna tafiya kafada da kafada da maki 17.

Amma RB Leipzig na a matsayi na 10 da maki 15 bayan nasarar da ta samu a kan Hertha Berlin da ci 3-2. Ita kuwa Mainz ta bi Werder Bremen har gida kuma ta lallasa ta da ci 2-0 a wasan da muka gabatar muku kai tsaye a ranar Asabar. A karshe Stuttgart ta doke Bochum da ci 4-1.

Hukumar kwallon kafa ta Asiya ta sanar da Qatar a matsayin kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin wannan nahiya a shekara ta 2023, bayan Chaina ta sanar da janyewarta a watan Mayun da ya gabata sakamakon yaduwar cutar corona. Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a cibiyarta da ke Malaysia ta ce, Qatar ta fi kasancewa cikin shiri fiye da kasashen Koriya ta Kudu da Indonesiya da suka shiga takara, sakamakon bakuncin gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2022 da za ta yi a watannin Nuwamba da Disamban 2022. Za a gudanar da gasar kwallon kafa ta kasashen Asiya a Qatar a 2023 watanni kalilan bayan da ta dauki bakuncin kofin duniya.