Labarin Wasanni 14.11.2022
November 14, 2022Shahararren dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa kungiyarsa ta ci amanarsa. Ronaldo ya fadi haka ne a wata hira ta musamman da ya yi inda ya yi kalamai masu zafi a kan Man U da kuma kococinsa. A lokacin da ya tabo batun tsohon kocin rikon kwarya na kungiyar Rangnick, ya ce bai cancanci zama kocin Manchester United ba saboda bai taba ma jin labarinsa ba.
Da kuma aka yi masa tambaya game da kocinsa na yanzu Ten Hag, Ronaldo ya ce ba ya girmama shi saboda shi ma ba ya girmama Ronaldo. Daga bisani kuwa da aka yi masa tambaya game da yadda tsohon abokinsa Rooney yake caccakar sa, sai Ronaldo ya ce bai san dalilin da ya sa yake sukarsa ba, sannan ya kara da cewa watakila saboda ya yi ritaya ni kuma har yanzu ina taka leda a babban matakin."
Wannan dai hirar ta jawo cece-kuce sosai tsakanin ma'abota kwallon kafa, inda wasu ke ganin bai kamata ya fito ya yi irin wannan maganar da ' yan jaridu ba. Abin jira a gani shi ne ko wadannan zafafan kalaman za su sa Ronaldo raba gari da kungiyarsa bayan an dawo daga gasar cin kofin duniya da Qatar za ta dauki bakunci.
Har yanzu muna Ingila, inda a gasar Premier League, Manchester City ta sha kashi a karon farko a gida a bana kuma a hannu Brentford (2-1) a ranar Asabar, don haka ta rasa damar karbe jagorancin gasar Premier daga hannun Arsenal. Manchester City dai ta yi rashin maki uku masu muhimmanci a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar 16 ga wata. A yanzu dai Gunners din na da damar da za ta jagoranci tazarar maki biyar, kafin hutun makonni shida na gasar cin kofin duniya, idan har ta samu nasara a filin wasan.
Yanzu kuma sai Jamus, inda Bayern Munich ta ci gaba da zama a saman teburin Bundesliga bayan da ta doke Schalke 04 da ci 2-0 a mako na 15, yayin da RB Leipzig ta haye matsayi na uku na wucin gadi bayan da ta mamaye Werder Bremen da ci 2-1. Wannan dai ita ce nasara ta biyu a jere da Yaya-babba mai maki ta samu, lamarin da ke nuna cewa ta koma kan ganiyarta bayan jinkiri na watan Satumba. Yayin da Leipzig ta gudanar da wasanni takwas ba tare da an doke ta ba, saboda haka ta samu ratar maki shida da Bayern.
Daga yanzu dai an dakatar da gasar Bundesliga sakamakon gasar kofin duniya da za a fara a ranar 20 ga wannan wata na Nuwmba a kasar Qatar. Za a dora ne a 15 ga watan janirun 2023 idan Alah ya kaimu, inda za a fuskanci karon batta tsakanin RB Leipzig da Bayern Munich.
Kwanaki shida suka rage a fara gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ta fi janyo cece-kuce a tarihi a karkashin bakuncin Qatar. Sai dai kasar na da tarin tabargaza da ta yi da ta shafa mata kashin kaji, kama daga batun FIFA har zuwa wuraren gine-ginen gasar cin kofin duniya, sannan ga batun take yanayin 'yancin dan Adam. Yanzu haka shirye-shiryen karshe sun kankama. Kasashe biyar ne za su wakilci nahiyar Afirka a kafin na duniya ciki har da Kamaru da Ghana da Senegal da maroko da Tunisiya.
Daga wannan Litinin muke fara gabatar muku da rahotanni game da shirye-shiryen kofin duniya, kuma za mu bayyana muku wainar da za a toya a fagen wasanni daga ranar lahadi mai zuwa.
Kungiyar ASFAR ta Maroko ta lashe gasar cin kofin zakarun kwallon kafa na mata a karon farko, bayan ta doke Mamelodi Sundowns da ke rike da kofin da ci 4-0 a gasar Maroko. Dama dai 'yan wasan kasashen biyu sun hadu a watan Yulin da ya gabata. Masu masauki na Maroko ne suka fara cin kwallon farko a bugun fenarti a minti na 15 da fara wasa. Sai dai cire Yar wasan Sundowns da aka yi ya jawo wa kungiyar tra Afirka ta kudu rauni, lamarin da ya sa 'yan matakan Maroko samun gangara tare da kara wasu kwallaye uku.