1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labaran Afirka da suka dauki hankalin jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar ZMA
March 1, 2024

Yajin aiki Guinea da tsaurara hukunci ga ma su auren jinsi a Ghana da tasirin Erdogan a Afirka su ne suka dauki hankalin jaridun a wannan makon.

https://p.dw.com/p/4d4xh
Hoto: Hartmut Schmidt/imageBROKER/picture alliance

Bari mu fara da jaridar die tageszeitung da ta rubuta sharhinta mai taken: "Yajin aikin sai baba ta-gani ya kassara kasar Guinea. Kungiyoyin kdago na hada kawunan al'ummar kasar domin nuna adawarsu da gwamnatin mulkin soja." Jaridar ta ce mutane biyu sun halaka a Conakry babban birnin kasar, bayan da aka yi arangama tsakanin ma su zanga-zanga da jami'an tsaro wadnada suka yi amfani da barkonon tsohuwa da harsasai ma su rai domin tarwatsa dandazon ma su zanga-zangar karkashin kungiyar kwadagon kasar CNTG. Tun dai a ranar Litin din da ta gabata new, aka rufe ba ki dayan birni tare da sanya shingaye a babban titin Le Prince. An yi arangama a yankuna na birnin Sinfonia. Kakakin kungiyar kwadagon, ya bayyana cewa kisan mutanen biyu ka iya ta'azzara al'amura. Ta ce batun kamewa tare da yanke hukuncin watanni shida a tsare ga sakataren kungiyar 'yan jaridun kasar ta Guinea Sekou Jamal Pendessa ne, ya janyo yajin aikin da tuni ya samu goyon bayan jam'iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula. Suma bankuna da kasuwanni da makarantun da gidajen mai da kuma shaguna, sun ci gaba da kasancewa a rufe.

Pro-Putsch-Demo in Nigers Hauptstadt Niamey
Hoto: AFP

Majalisar dokokin Ghana ta tsaurara hukunci ga ma su auren jinsi, in ji jaridar Zeit Online a sharhinta mai taken: "LGBTQ duk wanda ya bayyana kansa a matsayin dan luwadi ko madigo ko kuma wani abu makamancin hakan, ka iya fuskantar barazanar daurin shekaru a gidan kaso ba da jimawa ba. Ma su kare hakkin dan Adam, sun yi tir da wannan al'amari. Jaridar ta ce 'yan majalisar dokokin Ghana sun amince da wani kudurin doka, wanda ya tanadi hukunci mai tsauri ga masu auren jinsi da dangoginsu. Haka ma duk wanda ya nuna goyon ba ya ko ya taimaka musu, zai dandan kudarsa. Kudurin dokar da majalisar dokokin Ghana ta amince da ita a Larabar wannan makon dai na dakon sanya hannun shugaban kasar Nana Akufo-Addo da aka taba jiyo shi yana cewa,zai sanya hannu a kai in har mafi yawan al'ummar kasarsa abin da suke so ke nan. Tun bayan gabatar da kudirin dokar a majalisar dokoki tsawon shekaru ukun da suka gabata, kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke zanga-zanga a kanta. Sai dai kuma dokar, ta samu goyon bayan malaman addinai da sarakunan gargajiya.

Somalia, Mogadishu | Soldaten während eines Trainings
Hoto: Ercin Erturk/AA/picture alliance

Za  mu karkare da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a sharhinta mai taken: "Tasirin Erdogan a Afirka, yadda Turkiyya ke tallafawa sojojin Somaliya ba da jimawa ba jiragen ruwan yakinta za su fara bai wa Somaliya kariya." Jaridar ta ce tuni gwamnatocin kasashen biyu suka amince. Turkiyya na fadada ayyukan sojanta a yankin Kahon Afirka, karkashin yarjejeniya. Yarjejeniyar da ta zamto abin mamaki ga ma su sanya idanu da dama, za kuma ta iya zama wani matakin Somaliya na raya kasashe da kuma martani kan matakin yankin Somaliland na kulla alaka da Habasha da Mogadishun ke masa kallon barazanar siyasa. Kan yarjejeniyar Habashan da yankin Somaliland da suka cimma a ranar daya ga watan Janairun bana dai, Somaliyan ta samu goyon baya daga wasu kasashen Afirka da na Larabawa. Haka kuma Tarayyar Turai EU ta soki wannan alaka, tare da yin kira da a girmama hadin kan Somaliyan.